Mawuyacin halin da ake ciki a Bangui | Labarai | DW | 20.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mawuyacin halin da ake ciki a Bangui

Shugabar hukumar kare hakkin bani Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ta ce ta kadu matuka game da halin da al'ummar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ke ciki.

Navi Pillay

Shugabar hukumar kare hakkin bani Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay

A jawabinta ga manema labarai a birnin Bangui, Ms Pillay ta ce duk da dai yanayin da kasar ke ciki a watannin baya ya sha banban da na yanzu, amma ya zuwa yanzu ba a daina kashe-kashe ba musamman ma dai irin wanda 'yan anti-Balaka ke yi.

Pillay ta kara da cewar har yanzu akwai tsananin gaba tsakanin musulmi da kirista, wanda ya sanya wasu musulmin kasar kimanin dubu 15 ke makale a wasu sassa na arewacin kasar don tsira da rayukansu ko da dai suna samun kariya daga dakarun kiyaye zaman lafiya.

Wani abu mai tada hankali inji jami'ar shi ne yadda ake samu karuwar laifuka na fyade a kasar, baya ga matsanancin halin da yara kanana ke ciki da ma talaucin da ya yi wa wannan kasa mai dumbin arzkin karkashin kasa dabaibayi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar