Matsin lamba kan ′yan Kataloniya | Labarai | DW | 09.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsin lamba kan 'yan Kataloniya

Shugaban yankin Kataloniya da ke rajin ballewa daga kasar Spain na cigaba da fuskantar matsin lamba kan ya jingine shirin da ya ke shi da al'ummarsa na girka kasarsu mai cin gashin kai.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce maimakon wannan yunkuri na ballewa kamata ya yi bangarorin biyu su hau teburin tattaunawa don kawo karshen banbance-banbancen da ke tsakaninsu. Shi kuwa Emmanuel Macron da ke jagorantar Faransa a nasa bangaren cewa ya yi kasarsa ba za ta taba goyon bayan 'yan Kataloniya ba muddin suka yi gaban kansu wajen ballewa daga Spain. A gobe ne dai ake sa ran shugaban na Kataloniya zai yi jawabi ga majalisar dokokin yankinsu kuma ana kyautata zaton batun ayyana 'yancin cin gashin kai ne zai zama jigon jawabin nasa, lamarin da ya tadawa mahukuntan Madrid hankali.