Matsin lamba ga Jacob Zuma don ya sauka | Siyasa | DW | 15.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsin lamba ga Jacob Zuma don ya sauka

Kira na neman shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya sauka daga mukaminsa na ci gaba da karuwa bayan sauya ministocin kudi kasar har so uku cikin mako guda.

Saurari sauti 03:14

Rahoto kan kira ga shugaba Zuma da ya sauka daga mukaminsa

Shugaba Zuma ya sauke ministan kudi Nhlanhla Nene tare da maye gurbinsa da wanda bai da kwarewa David Van Rooyen. Sannan kwana hudu ya sake cireshi da maye gurbinsa da tsohon ministan kudi Pravin Gordhan. Hakan dai ya sanya suka ga gwamnatinsa, da ma sanya kudin kasar wato Rand ya fadi kasa. Sannan aka shiga rudani kan makomar tattalin arzikin wannan kasa ta Afirka ta Kudu, batutuwan da suka sanya kiraye-kirayen ya sauka daga kujerar da shugaba Zuma ke jagoranta.

Max Du Preez, marubuci ne wanda kuma kan yi sharhi kan lamuran da suka shafi siyasar kasar ta Afirka ta Kudu. Ya na mai ra'ayin cewa shugaba Zuma a yanzu ya zamewa kasar matsala wacce ke barazana ga rayuwar mutane miliyan 50.

Ya ce " ina zaton mulki ya sa ya rude da zama mai babakere a harkar da ta shafi rashawa, ya na yaudarar kansa kan abubuwan da baya iya hangensu."

David Douglas Des van Rooyen Finanzminister Südafrika

David Douglas Des van Rooyen na daga cikin ministocin da aka sauke saboda rashin kwarewa

Duk da gaggauta yin gyara ga wannan abu da masana ke yi wa kallon tabargaza ga tattalin arzikin Afirka ta Kudu, a ranar Lahadi shugaba Zuma ya cire Van Rooyen da mayeshi da Pravin Gordhan tshohon ministan kudi. Wani abu da ya dan farfado da darajar ta kudin kasar Rand. A ranar Litinin Gordhan ya ba wa al'ummar kasar tabbaci cewa komai ya koma kan turba.

Ya ce "za mu maido da martabar harkoki da suka shafi kudaden, zamu fitar da sabbin tsare-tsare da kawar da kai ga wasu batutuwa da ba su zama tilas ba dan ba wa wadanda zasu habbaka tattalin arzikinmu fifiko da zuba jari a harkar da ta shafi tattalin arziki."

 Alkawuran sabon ministan kudin Afirka ta Kudu

Sabon ministan ya ba wa masu zuba jari tabbaci na basu kariya da ma ba wa duk harkokin da suka shafesu kariyar da ta dace a kasar ta Afirka ta Kudu. Sai dai a fadar Abdul Waheed Patel wani mai sharhi kan lamuran da suka shafi siyasar kasar ta Afirka ta Kudu abin da shugaban ya yi shi ne daidai.

Ya ce "ba na jin abu ne na kwana guda, abu na farko shi ne a yi kokari a cire tsoro da masu zuba jari da ma wadanda ke son zubawa a kasar ke da shi duka kuwa na cikin gida da ma na kasa da kasa."

Kafafan yada labarai a a kasar ta Afirka sun baza bayanai dai a ranar Litinin inda al'umma da dama ke ta neman shugaba Zuama ya bar kujerarsa. Pakiswa William Kalane wani dan kasar ne mai shekaru 28 da haihuwa na da irin wannan ra'ayi.

Südafrika Proteste gegen die Korruption

'Yan Afirka ta Kudu sun sha alwashin ci gaba da neman Zuma ya sauka daga mukaminsa

Ya ce "zai fi kyau idan zamu sami wani matuki da ya dace kada ya bari wannan jirgi ya nitse. Abu ne da ya fi dacewa, Zuma ya koma kan batun kiwon shanu da kajinsa a Nkandla wannan abu ne da bai shafi kasar nan ba."

Sai dai duk da wannan suka jam'iyyar ANC mai mulki ta ce dari bisa dari ta na tare da shugaban kasar. Zizi Kodwa shi ke magana da yawun jam'iyyar ta ANC.

Ya ce "jam'iyyar ta ANC na da karfin gwiwa a kan shugaba Zuma, shugabanci karkashin Zuma shi ne abin da bamu da haufi akai."

Wadanda ke son shugaba Zuma ya sauka daga mulkin wannan kasa sun shirya gudanar da maci a ranar Laraba a gaban ginin fadar shugaban ta Union Buildings yayin da 'yan adawa daga jami'iyyar AD ke neman 'yan majalisa su zauna a watan Janairu don kada kuri'ar cireshi daga kujerar mulkin kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin