Matsi ya sa an saki dan fafutuka a Aljeriya | Labarai | DW | 31.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsi ya sa an saki dan fafutuka a Aljeriya

Dan fafutikar Aouf Hadj da Kameleddine Fekhar da ya rasu a tsare an kama su a watan Maris saboda adawa da manufofin gwamnati da ma na sojan Aljeriya.

Mahukuntan kasar Aljeriya sun saki dan fafutikar nan Aouf Hadj bayan kwashe watanni uku a gidan kaso kamar yadda lauyansa ya bayyana a wannan Juma'a. An dai saki Hadj, dan shekaru 49, daga gidan kaso na lardin kudancin Ghardia a ranar Alhamis kamar yadda lauya Salah Dabou ya bayyana a shafin Facebook.

Sakin nasa dai na zuwa kwanaki bayan da abokin gwagwarmayarsa Kameleddine Fekhar ya rasu a gidan kaso sakamakon yajin kin cin abinci. Lamarin da ya jawo zanga-zanga da ma tofin alatsine na 'yan fafutika.

Dukkaninsu dai Fekhar da Hadj an kama su a watan Maris saboda sukar mahukunta ciki har da sojoji kamar yadda 'yan fafutika suka bayyana.