Matsayin sojan Faransa a Bangui | Labarai | DW | 02.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsayin sojan Faransa a Bangui

Sojojin Faransa da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, za su yi aiki ne na wani gajeren lokaci

Kasar Faransa ta bayyana cewa tura dakaru da ta yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bawai na har abada bane. Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian, shi ne ya bayyana hakan a wata ziyarar da ya kai a Bangui babban birnin kasar a yau. Dian ya ce "dama mun fadi haka a lokacin da muka tura dakarun mu a kasar Mali, kuma a nan ma, zan sake jaddawa, mun zo ne kawai domin taimakawa dakarun kasashen Afirka da ke aikin kiyaye zaman lafiya, domin tab batar da doka da oda". A watan jiya ne dai kasar Faransa ta tura sojoji 1600, izuwa kasar da Faransan ta yi wa mulkin mallaka, bayan tashe-tashen hankula wadanda suka biyo bayan kifar da gwamnatin Bozize. Kasar Faransa dai, ta yi kokarin ganin an samu kudurin MDD na tura dakaru a Bangui, amma ta kasa samun nasara wajen jawo hankalin kasashen Turai, da su aika da sojoji, illah kawai akasarin kasashen na Turai sun yi alkawari bada kayan aiki ne.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasiru Awal