Matsayin rawani ko hula a addinai a sassa na duniya
Mabiya addinai a duniya kan yi amfani da nau'uka na mayafin kai da ke nuna kamala da kwarjini. Yahudawa a wasu kasashe da masu bautar Mithra a daular Rumawa na cikin masu amfani da kyallaye na alfarma a matsayin rawani.
Yarmulke
Yahudawa da ke nahiyar Turai sun fara sanya hular Yarmulke ko Kippa ne tun cikin karni na 17 zuwa 18, abin da ke zama muhimmiyar alama ta addini. Ana sa ran wadanda suka yi imani su rika sanya hular lokacin addu'o'i. Haka nan ma an amince da amfani da mayafin kai. Dokar Yahudawa ta amince wa maza ne su yi hakan a wuraren bauta ko makabartu.
Miter
Hular miter, hula ce ta bukukuwa na musamman da manyan Bishop na darikar Katholika cikin Kiristoci ke amfani da ita. An soma amfani da hular tun a karni na 11, wadda tsinin tsakiyarta ta rabe gefen hagu da kuma dama, wanda ke matsayin yanda sabo da kuma tsohon alkawari yake cikin littafin Linjila wato Bible.
Dastar
Nan kuma rawani ne na mabiya addinin Sikh na yankin arewacin Punjab na kasar Indiya. An fara amfani da rawanin ne a cikin karni na 15. Maza ne ke amfani da kyalle mai ruwan goro da aka fi amince masa. Daga kasanshi kuma akwai wani yadin wanda ake dinke shi a kowace safiya kafin a sanya. Maza mabiya wannan addini kan bar gashin kansu ya girma kwarai ba tare da sun yanke ba.
Chador
Farisawa na amfani da kalmar Chador da ke nufin rumfa ko tanti. Haka nan kalmar ta wani kyalle ce da mata Musulmai na yankin Gabas ta Tsakiya ke amfani da shi. Kyalle ne baki akasari matan ke sanyawa daga saman kai har ya zuwa idon sawu. Suturar na kare bayyanar surar jikin matan, in baya ga fuska. Ana amfani da shi a matsayin sutura ta yau da kullum.
Nun's veil
Mata masu bauta da ake kira Nun, na amfani da kyallaye na musamman don samun kamala ta addini a kusan kullum. Sabbin shiga daga cikinsu na sanya ratsin fari, yayin da wadanda suka jima ke amfani da baki ko launin da ya dace da dabi'arsu. Kyallayen na zuwa ne cikin launuka da tsawo gami da tsari na dinki. Wasunsu na rufe kan matan, sai kuma wasu da ake likawa da gashin "Sista".
Headscarf
Shin wai nikabi kam sutura ne na addini ko kuma wata hanya ce ta tauye 'yancin mata? A kasashen yamma musamman, wannan batu ne da ake ta muhawara a kansa. Nikabin dai nau'i ne na sutura da ya yi fice a bangaren mata Musulmai. A wannan hoto, wata 'yar Turkiyya ce ke sanye da nata. Matan Larabawa na sanya suturar cikin launi da tsari kala-kala.
Sheitel
Nan, matan Hasidi da ke cikin al'umar Yahudawa mazauna New York na Amirka ne. Suna da tsauraran dokoki kan matan aure, da ake tilasta su yanke gashin kansu suna dora farin gashin kanti da ake yin kari da shi mai suna "Sheitel." A cikin wani littafin da ta wallafi da ya sahara, marubuciya Deborah Feldman, ta yi bayanin yadda ta taso cikin kungiyoyi na addini.
Birett
Manyan limaman Katolika na kasashen Jamus da Holland da Birtaniya da Faransa, suna amfani da wannan nau'i na hula ta addini. An yi hular ne da jan kyalle da ake dorawa kan wata takarda mai kauri inda a karshe take daukar wannan surar. Cikin karni na 13 ne aka fara hulunan masu kwanoni hudu, amma a wasu kasashen, kwanoni uku ne ake yin su.
Tagelmust
Wasu musulmai a gabashin Afirka na amfani da kyalle da a wani kaulin ke kaiwa mita 15 da suke rawani da shi. Buzaye a nahiyar, na amfani da tsarin wanda suke zagaye kai da baki da hanci da shi saboda kariya daga rairayin hamada. Galibi manya ne ke rawanin. Wasu ma daga cikinsu na amfani da launin shudi da aka san mazan yankin na hamada da shi.
Shtreimel
Wannan ma wata hula ce ta Yahudawa wacce ake yin ta da karammiski wato velvet. Maza magidanta ne ke sanya ta lokacin hutu da bukukuwa irin na addini. Tushen hular mai jan hankali, ya samu ne daga al'umar Hasidi da ke a Kudu maso Gabashin Turai. Sai dai al'ada ce ta ta bace a Turan bayan kisan kiyashi da aka yi wa Yahudawan.
Hats and bonnets
Kiristoci masu ra'ayin rikau da ke arewacin Amirka masu tsatso daga darikar Baptist ta Ana na kasashen Switzerland da kudancin Jamus ne a nan. Wadannan mutane sun yi hijira ne a farkon karni na 18 inda suka guje wa zalunci irin na addini. Suna can suna rike da rayuwar gargajiya ba tare da kayan zamani ba. Su kan sanya hular malafa mazansu da matansu.