1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya a cin hanci da rashawar duniya

Uwais Abubakar Idris YB
January 29, 2019

Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta Transparency International ta fitar da rahotonta ga yadda kasashe suka kasance a kan batun cin hanci da rashawa a 2018 inda ta nuna cewa a Najeriya babu wani sauyi.

https://p.dw.com/p/3CNMw
Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Rahoton na kungiyar ta Transparency International da ya yi nazari a kan kasashe 180 a duniya ya nuna yadda wasu kasashe da dama suka kara fuskantar matsalar cin hanci da rashawa, yayin da kalilan suka samu ci gaba. Sama da kashi biyu bisa uku na kasashe sun sami kasa da maki hamsin cikin dari, abin da ya nuna bayyanar matsalar.

Rahoton ya nuna cewa Denmak ce ta farko a kasashen duniya da ba su da cin hanci da rashawa, amma Najeriya ta samu maki 27 bisa dari inda ta zama kasa ta 144 daga kasashe 180 masu matsalar cin hanci da rashawa idan aka duba adadin makin da ta samu a shekara ta 2017.

Cartoon: Buhari-CJN Anklage
Masu shari'a ma ba su tsira ba a zargin cin hanci

A Afirka dai akwai kasashen da suka samu ci gaba sosai a wannan batu na yakar cin hanci irin na Seychelles da Ruwanda da Botswana, domin sun samu fiye da maki hamsin . To amma yaya za’a ce Najeriya ba ta samu ci gaba ba kasancewar a 2017 tana matsayi na 148 ne a yanzu kuma ta matsa zuwa 144 duk da cewa makin da ta samu iri guda ne? Mr Okeke Anya jami'in kungiyar ne mai kula da mulki bisa kamanta adalci ya ce Najeriya ba ta hada makin da ake bukata ba wajen samun ci gaba.

Kungiyar CISLAC dai ta danganta cin hanci da tabarbarewar dimukurdiyya a kasashen da matsalar tafi muni. Ko wacce shawara suke bayarwa don kara kaimi a yakar masu halin bera?. Halimatu Nuhu Isa ita ce jami’a mai kula da yakar cin hanci a kungiyar ta CISLAC: “Kamata ya yi a rika ba wa 'yan jarida karfin gwiwa haka kungiyoyi masu yaki da cin hanci, sannan gwamnati ta tashi tsaye."

A  baya dai Najeriyar kan yi koken cewa rahoton kungiyar ba na gaskiya ba ne bisa zahirin abubuwan da ke faruwa a kasar saboda irin makudan kudaden da ta karbo da ma nasarorin da ta samu na yakar masu halin bera a kasar, to sai dai kungiyar na cewa hasashen da take bisa gaskiyar abubuwan da ke faruwa ne kuma babu dalilai na siyasa a ciki.