Matsayin Jamus kan turawa da sojoji Mali | Labarai | DW | 23.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsayin Jamus kan turawa da sojoji Mali

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce kasarsa ba za ta bayar da gudunmawar makamai da sojoji domin yakar 'yan ansruddina a arewacin Mali ba.

Ministan harkokin wajen Jamus ya ce kasarsa a shirye ta ke ta bayar da gudunmawa wajen inganta harkokin tsaro a kasar Mali. Sai dai ya ce ba za ta bayar da gudunmawar makamai ko na sojoji domin fatattakar masu kaifin kishin addinin musulunci daga arewacin kasar ba. Guido Westerwelle ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana a birnin Berlin da manzon musamma na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali Romano Prodi.

Manyan jami'an biyu sun tattauna game da tallafin da Jamus za ta bayar wajen koya wa jami'an tsaron kasar Mali dabarun yaki. D am tun a jiya litinin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana hanyoyin da karsata za ta bi wajen taimaka a warware rikicin na Mali.

Kasashe da suke makobtaka da ita Mali ciki har da Mauritaniya da Algeriya na nuna dari dari game da daukan matakan soje akan 'yan Ansaruddine. Yayin da su kuma kasashen yammacin duniya ke nuna fargaba game da rikedewar arewacin Mali zuwa sansanin kulla ayyukan ta'addanci a Afirka. Majalisar Dinkin Duniya na jiran kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta yi mata bayyani dalla dalla game da hanyoyin da za ta bi wajen karbe arewacin Mali daga hannu masu tsananin kishin addinin musulunci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal