Matsayin arewacin Najeriya a sha′anin man fetur | Siyasa | DW | 28.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsayin arewacin Najeriya a sha'anin man fetur

Duk da ci gaban da aka samu a batun hako man fetur a yankin arewa, amma ana cece kuce akan sake fasalin sashen man fetur na kasar.

Majalisar kula da tattalin arziki kasa ta yankin arewacin Najeriya tace gwamnatin tarayyar kasar ta samar da kudi dalar Amirka miliyan 100 a shekarar da muke ciki domin ci gaba da ayyukan bincike don fara hako albarkatun mai a wasu sassan yankin.

Za’a yi amfani da wadannan kudade ne domin fadada bincike tare da yin nazarin hanyoyin da za’a bi wajen fara hako man musamman a gabar tafkin Chadi da na kogunan Benue da Bidda da Kogin Rima a jihar Sokoto da ma sauran wurare da ake zaton akwai albarkatun man a yankin Arewacin Najeriya.

Koda a shekarun da suka wuce dai gwamnatin ta samar da makudan kudade don aikin binciken sai dai yanzu haka bata fara cimma ruwa ba dangane da shirin fara hakar man.

Dama dai gwamnatin ta dade ta na bayyana aniyar fara aikin hako man a arewacin Najeriya tare da ware makudan kudade da nufin samun nasarar wannan shiri to amma tsawon lokaci har yanzu babu abinda aka yi akai abinda ake ganin an sa siyasa a ciki.

Wannan ya sa masana da masharhanta ke ganin akwai wata manufa dake boye in aka duba irin tafiyar hawainiya dangane da wannan aiki na hako albarkatun mai a yankin Arewacin Najeriya.

Ra'ayoyin 'yan Najeriya akan batun hako man fetur

Alhaji Adamu Adamu mai dala wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya.

Talakawan wannan yanki kuma na ganin ana neman gina wasu ta wannan hanyar musamman ganin yadda cin hanci da baba-kere ke taka muhimmiyar rawa tsakanin manyan Najeriya.

Duk da sanin muhimmanci da kuma amfanin da wannan mai zai yiwa yankin arewacin Najeriya da aka yi imanin shi ne mafi koma baya tsakanin sauran yankunan kasar wasu na ganin kamata yayi gwamnatin ta maida hankali wajen bunkasa ayyukan noma da aka san yankin na da shi.

Dr Sadiq Umar Abubakar yana cikin masu wannan tunani.

Shugaba Goodluck Jonathan dai yayi alkawari a lokacin yakin neman zabe da ma ziyarar baya-bayan nan da ya kai yankin arewa maso gabashin Najeriya cewa zai tabbatar da fara hako man cikin kankanin lokaci, sai dai lokaci kawai zai iya tabbatar da hakan.

Mawallafi : Al-Amin Suleiman Muhammad
Edita : Saleh Umar Saleh