1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsayar EU kan makomar Venezuela

Yusuf Bala Nayaya
February 8, 2019

An dai ga wasu motoci na dakon kaya biyu makare da kayan agajin da suka hadar da abinci da magunguna sun shiga birnin Cucuta na Kwalambiya wanda kogi ne ya raba shi da kasar ta Venezuela.

https://p.dw.com/p/3Cylb
Montevideo Treffen Venezuela Konferenz
Federica Mogherini a gaba lokacin da ta isa taro kan VenezuelaHoto: Getty Images/AFP/P. Porciuncula

Kungiyar Tarayyar Turai dai ta goyi baya na shirin tattaunawa da ma kira na gudanar da zabe a kasar ta Venezuela kana ta yi kira na janye jiki na kutse kan harkokin siyasar cikin gidan wata kasa. Kungiyar ta bayyana haka bayan zama da jakadu daga kasashe 13 daga yankin Latin Amirka a Yurugai.

Manyan motoci makare da kayan tallafi da Amirka ta shirya za su isa kasar Venezuela. A ranar Alhamis sun isa iyaka da kasar Kwalambiya, abin da ke zuwa bayan da 'yan adawa suka sha alwashi na shiga da su kasar da ke halin tsaka mai wuya, duk kuwa da sukar matakin kai kayan agajin da Shugaba Nicolas Maduro mai fama da kalubale na shugabanci ya yi.

Yanzu dai hankali ya karkata kan ganin matakin da Maduro zai dauka ko zai bari kayan su shiga kasar ko kuwa ya hana? Ya dai ki amincewa ma da halin tagayyara da kasar ta fada inda ya ce kasar ta Venezuela ba kasa ba ce ta mabarata ba.