Matsalolin tsaro a Tuddan Golan | Siyasa | DW | 25.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalolin tsaro a Tuddan Golan

A wannan larabar ce ake sanar da fadada wa'adin ayyukan sojojin sa ido a tuddan Golan da ke kan iyakokin Israela da Siriya. Sai dai akwai ayar tambaya.

Tun daga lokaci mai tsawo ne dai Majalisar Dinkin Duniya take da rundunar kwance damara da ake kira UNDOF a takaice, da ke tafiyar da ayyukansu cikin tsanaki a tuddan Golan. Rundunar MDD na aikin sa ido ne kama daga shekara ta 1974, daga tazarar kilomita 70 domin tabbatar da daraja wa shirin kwance damarar yaki tsakanin Izraela da Siriya.

Da barkewar yakin basasa a Siriya dai, kan iyakarta da Izraela da ya kasaance cikin lumana na tsawon shekaru na fuskantar matsaloli. Ana samun barazana dangane da yadda sojojin gwamnatin Siriya ke ci gaba da arangama da mayakan tawayen kasar, musamman ma ta wadannan yankuna, wanda ya jagoranci bude wuta daga Izraela. A watan mayun da ya gabata ne dai, sojojin Philippin da ke aiki a tuddan suka fada hannun 'yan tawayen Siriya. Kazalika irin wannan rikicin ne ya sa kasar Austria ta sanar da janye dakarunta daga yankin. Gwamnatin Austrin dai ta bayyana hatsarin ci-gaban kasancewar sojojinta a yankin.

A picture taken from the Israeli side of the Israel-Syria ceasefire line in the Golan Heights shows ashes in a minefield set off by stray mortar bombs fired during fighting between forces loyal to the Syrian regime and rebels opposed to Syrian President Bashar al-Assad near the Quneitra border crossing between Israel and Syria on June 7, 2013 .AFP PHOTO / AHMAD GHARABLI (Photo credit should read AHMAD GHARABLI/AFP/Getty Images)

Tuddan Golan

Yanzu haka dai yiwuwar fadada wa'adin ayyukan Sojojin MDD a tuddan na Golan, da ake saran kasancewa a ranar 26 ga watan Yuni, na fuskantar barazana da wannan sauyi da aka fuskanta, na janyewar sojin Austria daga runduwar. Shin akwai yiwuwar cimma burin fadada wa'adin? Amsar dai ita ce, ko kadan a cewar Heinz Gärtner, farfessa a cibiyar nazarin siyasar kasa da kasa da ke birnin Vienna.

" Ya zamanto wajibi a sauya yadda wa'adin zai kasance, domin rundunar ta iya kalubalantar duk wani kutse da sojojin Siriya za su iya yi a yankin tafiyar da ayyukansu". A cewar Farfesan kimiyyar siyasar dai, hakan ya zamanto batu na gaggauta daukar mataki. Kasancewa a yanzu haka rundunar MDD na aikin sanya idanu ne kawai a tuddan Golan, suna sa baki ne kawai idan akwai bukatar matakan ko ta kwana na kare kansu.

Babu wani shakku dangane da irin muhimmancin kasancewar sojojin a yankin, musamman kuma a wannan lokaci. Hakan ne ma ya sa MDD ta sanar da kara yawan sojojin daga 900 zuwa 1,250. Ayar tambaya a nan dai ita ce, shin wa zai maye gurbin rundunar Austria da ta janye? Wannan dai babbar matsala ce da ke gaban babban sakataren MDD Ban ki-moon, na maye gurbin sojin Austria 380. Tsibirin Fiji dai sun yi alkawarin maye gurbin sojin Austria. Yanzu haka za'a aike da sojjojin da aka yi musayarsu a da sojojin kasashen Kroatia da Japan da Kanada, wadanda suka janye dakarunsu tun daga farkon wannan shekara.

Ayyukan kiyaye zaman lafiya dai yana da muhimmanci ga kasashen da ke da raunin tattalin arziki. Domin kudaden da za'a biyasu, zai shige wanda suke samu a kasarsu ta asali, kazalika hakan yana kara wa irin kasashen farin jini ta bangaren manufofinsu na ketare. Hakan ba zai kasa nasaba da dalilan da suka da ake samun gudunmowar mafi yawan sojoji daga yankin Asia kamar Philippin da Indiya da Bangladash ko Pakistan ba.

A UN peacekeeper (top L) uses his binoculars on an observation tower in the largely abandoned city of Quneitra, in the demilitarized United Nations Disengagement Observer Force (UNDOF) zone, in the Golan Heights on March 8, 2013. The Philippines said on March 8 that rebels who are holding 21 Filipino peacekeepers hostage in the Golan Heights are insisting Syrian troops leave the area before releasing their captives. AFP PHOTO/JACK GUEZ (Photo credit should read JACK GUEZ/AFP/Getty Images)

Aikin sa ido a tuddan Golan

A cewar kwararren MDD Andreas Zumach dai, majalisar ta duka ka'in-da-na'in wajen samun mai maye gurbin Austria. Kawo yanzu dai babu nasara dangane da tattaunawarta da kasashen Sweden da Danemark. Bisa dukkan alamu dai za'a isa yanayin da babu wata kasar Turai da ke da wakilci a tsibirin Golan.

Ya ce" dalili kenan da yasa sakataren MDD ta kan yi tayi wa irin su tsibirin Fiji ko kuma wasu kasashe masu tarin matsaloli, wadanda ke shirye don aikin, koda yake basu da kwarewa dangane da ayyukan kiyaye zaman lafiya" .

Kwararru dai na ci gaba da bayyana muhimmancin kasancewar Sojojin kasashen Turai a rundunar MDD, wadanda ke tsaye kan kafafunsu, musamman bisa la'akari da cewar baya ga Siriya ita ma Lebanon na fuskantar barazana makamacin wanna.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin