Matsalolin talauci a Zambiya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 07.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Matsalolin talauci a Zambiya

Zambiya kasa ce da ke da dinbim arzikin tagulla ko jan karfe, amma al'ummominta na fama da talauci, yayin da cutar Ebola ta ke ci gaba da ta'adi a wasu yankuna na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

A cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung Zambiya kasa ce da ke da dinbim arzikin tagulla ko jan karfe, amma al'ummominta na fama da talauci. Yanzu haka dai aikin hakar tagulla ya koma hannun 'yan kasar Chaina lamarin da ya janyo fushin al'umma. Sai dai ana wannan kuma yanzu 'yan Chaina ne ke shirin sayen kamfanin samar da wutar lantarki na Zambiya. Taken Zambiya wadda ta samun 'yancin kanta daga Birtaniya a shekarar 1964 shi ne "Alfahari da 'Yanci", amma yanzu da yawa daga cikin 'yan kasar na zargin cewa kasar ta koma hannun 'yan Chaina. Masana na cewa tun kimanin shekaru 10 da suka wuce kasar da ke a matsayi na 10 a jerin kasashen da suka fi arzikin tagulla a duniya, ke fama da koma bayan tattalin arziki. Ga rashin iya shugabanci ga kuma uwa uba matsalar cin hanci da rashawa. Ana kuma zargin Chaina tana da hannu a cikin matsalolin da kasar ta samu kanta a ciki.

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Yuganda ne, tana mai cewa a bangaren kyautatawa da kuma daukar kaso mai yawa na 'yan gudun hijira kasar Yuganda ce ke a sahun gaba a nahiyar Afirka.

Jaridar ta ce a dangane da sassaucin manufofinta da suka shafi 'yan gudun hijira, Yugandar na samun taimako mai yawa daga kasashen duniya. To sai dai yanzu wani bincike na cikin gida da hukumkar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar, ya zargi hukumomi da aikata ba daidai ba, inda cin hanci da rashawa da sata suka mamaye tsarin karbar 'yan gudun hijira a kasar ta Yuganda. A farkon wannan shekara wani bincike da jaridar ta Die Tageszeitung ta yi, ta gano batutuwa na almundahana a ma'aikatar kula da 'yan gudun hijira ta Yuganda. Jaridar ta ce wannan babban abin kunya ne ga Yuganda da ake wa kallon abar koyi a kan batun 'yan gudun hijira.

A karshe sai jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi tsokaci kan cutar Ebola da ke neman gagarar kundila a wasu yankuna na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Ta ce fiye da mutane 400 suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, a dangane da yadda cutar ke yaduwa ya sa duk wasu matakan da ake dauka ba su yi tasiri ba. An ma jiyo wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiya na Kwango Richard Kitenge na cewa yanzu sun kai makura. Shi dai likitoci su na aiki ba dare ba rana don ganin an dakile yaduwar kwayoyin cutar ta Ebola. Kusan a kowane rabin awa jirgin saman daukar kaya na Majalisar Dinkin Duniya na tashi daga birnin Goma dauke da magunguna da mutane zuwa Beni da ke zama cibiyar annobar cutar.