1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

'Yan Salafiyya na kara zama barazana

Matthias von Hein ATB
October 22, 2018

A 'yan shekarun nan kungiyar Salafiyya ta yi karfi a yammacin Jamus musamman a jihar North Rhine Westphalia. Kungiyar wadda ke yi wa kanta lakabi da yada addinin gaskiya, kan raba kur'anai ga jama'a a manyan birane.

https://p.dw.com/p/36vKy
Demonstration islamischer Fundamentalisten in Solingen 01.05.2012
Hoto: picture-alliance/dpa/Melanie Dittmer

A cewar hukumar kare kundin tsarin mulki ta jihar North Rheine Westphalia fiye da mambobin kungiyar 250 sun zauna a yankunan yan gwagwarmayar Jihadi na IS. A shekarar 2016 ma'aikatar cikin gida ta Jamus ta haramta kungiyar saboda zargin 'yan kungiyar da kasancewa masu tsattsaurar akida. 

Tun bayan da aka haramta kungiyar ta Salafiyya, 'ya'yan kungiyar masu tsattsaurar akida suka kauracewa taruwa a bainar jama'a ammaba wai sun bace bane sun koma gudanar da ayyukansu ne a boye a cewar Kaan Orhon jami'i a hukumar yaki da tsattsauran ra'ayi Hayat da ke aiki a fadin Jamus.

"A bisa yanayi da tsarin rayuwarsu 'yan Salafiyya na tafiya ne a doron wa'azantarwa ta sanya mutum ya sauya daga addininsa ya karbi nasu. Ma'ana ta haka suke samun sabbin magoya baya. Suna kuma haka ne ta kafofin sadarwa kamar WhatsApp da kuma muhawara ta wasu kafofi wanda ya sa yake da wahala 'yan sanda da jami'an leken asiri su iya sa ido sosai kansu"

Kusan duk wadanda suka kai hare-hare a Jamus a baya bayan nan, mutane ne wadanda ke da alaka da kungiyar Salafiyya, misali Anis Amri wanda ya kai harin da ya hallaka mutane 12 a kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin a shekarar 2016.

Deutschland Salafismus Frauen
Hoto: picture alliance/dpa/U. Deck

Burkhard Freier jami'i ne a hukumar kare kundin tsarin mulki a jihar North Rheine Westphalia, ya ce halin da ke ciki a yanzu 'yan Salafiyya sun sauya salo ba sa bukatar kafa daula, suna rikidewa zuwa tsattsaurar akida a cikin gida.

"Yan Salafiyya na kara dunkulewa tare da sabbin mambobi. Suna haduwa a dakuna da bayan gidajensu inda suke kara yin karfi tun bayan haramta su da hukuma ta yi."

Sai dai kuma ba duk dan Salafiyya ba ne dan ta'adda amma duk 'yan ta'adda sun taba zama 'yan Salafiya a rayuwarsu a baya. Wannan ra'ayi ne da mutane wadanda suka yi mu'amala da masu bin tafarkin Salafiyya suka baiyana, kamar malaman makaranta a cewar Aziz Fooladvand.

"Yawancin yara da kan fada wannan tarkon basu ma san kansu ba, shin Bajamushe ne ni, ko musulmi ko kuma bako, ko dan kasar Turai. Wannan tambaya ce muhimmiya ga yara matasa."

Bildergalerie Islamismus in Deutschland
Hoto: picture-alliance/dpa/Britta Pedersen

Akwai dai banbanci a bisa manufa ta siyasa da kuma Salafiyya don Jihadi. 'Yan Salafiyya masu akidar Jihadi a shirye suke su yi amfani da tarzoma don cimma burinsu na kafa daular musulunci. Kashi 12 cikin dari na mabiya Salafiyya a jihar North Rhine Westphalia a Jamus mata ne wadanda suka je Siriya da Iraqi. Wannan dalili ne ya sa hukumomi suka sa ido akan irin wadannan mata da 'ya'yansu wadanda suka dawo bayan da aka murkushe yan IS. A yanzu irin wadannan yara suna makarantu a Bonn. Coletta Manemann jami'a mai kula da sajewar baki a Bonn ta ce akwai bukatar kulawa.

"A kullum idan aka sami iyalai sun sami kansu cikin wannan yanayi, hukumar kula da rayuwa da jin dadin matasa da kuma makarantu ya kamata su fadakar da su. A hannu guda kuma ya kamata mu baiwa wadanda suka dawo damar sajewa cikin al'umma. To amma kuma a waje guda dole ne mu kiyaye kada su sake komawa ga tsattsaurar akida."

Ita ma hukumar leken asiri ta kasar Jamus ta yi nuni da cewa 'yan Salafiyya na jan ra'ayin jama'a ta hanyar Itanet tare da cusa musu akidar don samun karin mabiya.