1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Matsalolin fadada kamfanonin Jamus a Afirka

Mohammad Nasiru Awal
September 7, 2018

Yunkurin gwamnatin Jamus na habaka huldar kasuwanci da kasashen Afirka na fuskantar wasu matsaloli kana Chaina ta yi Afirka alkawarin miliyoyi dubbai na dala ga Afirka lokacin taron kolin tsakanin bangarorin.

https://p.dw.com/p/34ThG
Republik Senegal - Kanzlerin Merkel besucht Senegal
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce gwamnatin Jamus ta yi kira ga kamfanonin kasar da su fadada aikace-aikacensu musamman jarin da suke zuba wa a nahiyar Afirka domin ta haka za su kirkiro da ayyukan yi a Jamus, sannan a lokaci daya za su kirkiro da miliyoyin guraben aiki a Afirka. Kana za a bude wa kasashen Afirka kofofin shiga da hajjojinsu a kasuwannin duniya. Za a samu karuwar yawan masu matsakaicin karfi da damar samun ilimi da kuma ba wa matasan nahiyar kyakkyawar makoma ta yadda ba sai sun dauki kasadar bi hanyoyi masu hatsari don shigowa Turai ba. Sai dai rashin tabbas na siyasa da yawan dogon turanci da rashin garanti na kare kudaden da kamfanonin Jamus din za su zuba a Afirka, na daga cikin kalubalen da shirin ke fuskanta.

China-Afrika-Gipfel in Peking
Hoto: DW/S. Mwanamilongo

Har yanzu dai muna kan batun huldar kasuwanci tsakanin Afirka da kasashen waje, inda a sharhi da ta rubuta jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce kasar Chaina na aike wa Afirka tsarinta na ci-gaban kasa.

Jaridar ta ce a taron kolin da ya gudana a farkon wannan mako tsakanin shugabannin Chaina da na kasashen Afirka a birnin Beijing, Chaina ta yi Afirka alkawarin miliyoyi dubbai na dala don yin manyan manyan ayyuka da za su samar da ci-gaba mai ma'ana a Afirka. Ko da yake a cewar jaridar wannan matakin da ma sauran ayyukan raya kasa da Chaina ta shafe shekaru tana yi a Afirka sun cancanci yabo amma babu cikakken bayani na ire-iren wadannan ayyukan raya kasa, ba a ma san wuraren da kudaden ke shiga ba ko ma wanda ke cin gajiyar jarin da ake sakawa. Sabanin kasashen yamma wadanda ke gindaya tsauraran sharudda kafin ba da bashi a Afirka, ita Chaina ba ta yi wa kasashen na Afirka katsalanda a harkokinsu na cikin gida.

Ita kuwa jaridar Der Taggesspiegel ta dubi halin da ake ciki ne a birnin Capetown na kasar Afirka ta Kudu tana mai cewa birnin na murnar samun ruwan sama bayan fari na tsawon lokaci da ya fuskanta.

Symbolbild - Kapstadt
Hoto: Getty Images

Ta ce yanzu dai ana iya cewa an kauce daga bala'in amma za a ci gaba da aiki da dokar ta-baci kan karancin ruwa a birnin. Jaridar ta ce duk wanda ya zagaya a birnin na Capetown a kwanakin nan zai ga yadda tafkuna suka cika da ruwa sannan a wasu wuraren ma har ambaliyar ruwa aka samu. Sai dai har yanzu ana aiki da dokar nan da ta takaita amfani da ruwa wadda aka kafa lokacin da birnin ya yi fama da matsalar kamfar ruwa mafi muni cikin shekaru 100.