1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalolin gyaran tsarin mulkin Najeriya

July 5, 2013

Kwamitin gyaran tsarin mulki Najeriya ya ba da shawarar cire kariya ga shugaban kasa tare da soke hukumomin zabe na jihohi. Sai dai masharhanta na ganin ba a nan matsalar take ba.

https://p.dw.com/p/192oR
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Kwamitin gyaran tsarin mulki na majalisar wakilan Najeriya ya gabatar da shawarwari masu yawa da yake ganin ya kamata a yi musu gyaran fuska, kama daga bai wa kanana hukumomi yancin cin gashin kansu har ma zuwa ga batun haramta rike mukamin gwamnati ga duk wanda ya taba aikata laifuffukan zabe. Abinda yafi daukar hankalin mafi yawan 'yan Najeriya a daukacin shawarwarin da kwamitin ya gabatar wa majalisar, shi ne batun cire kariyar fuskanatar shari'a ga shugaban kasa da matamakinsa da gwamnonin da mataimakansu a cikin Najeriya. Ana ganin cewar kariyar na basu ikon yin yadda suka ga dama da dukiyar kasa. Hon Musa Sarkin Adar ya bayyana dalilan da suka sanya suke ganin yin haka zai iya yin tasiri sosai.

Nigeria Präsident Goodluck Jonathan Beerdigung Autor Chinua Achebe
Wai shin Jonathan zai rasa rigarsa ta kariya?Hoto: Pius Utomi ekpei/AFP/Getty Images

‘'Cire wannan kariyar ita ce mafi amfani a Najeriya kuma ita ce za ta kara girmama demokaraudiyya a kasar nan. Idan mutum ya na ganin za'a iya tuhumarsa a kotu idan zai yi wani abinda ba dai-dai ba kuma ya tabbatar a zuciyarsa ba dai dai ba ne, kuma zai tozarta a kotu zai sa yaki yi wanan abin. Sannan idan ka bar wannan kujerar da ka ke a kanta shekaru hudu ko takwas za'a iya tuhumarka, to abin da dai ba ka iya kauce ma shi don me zaka ji tsoron a yi shi''.

Inda gizo ke saka game da tsarin mulkin Najeriya

Ko da yake 'yan majalisa na hangen tasirin da wadanan sauye-sauye ka iya yi a yunkuri karfafa mulkin demoukaradiyya a Najeriya, musamman batun soke hukumomin zabe na jihohi da a lokutan baya ake zargi da zama 'yan amshin Shata ga gwamnonin jihohin Najeriya. To sai dai ga Malam Abubakar Umar Kari masanin kimiyyar siyasa da zamantakewar al'umma na mai bayyana cewa baya ga karya tsarin demokaradiyya ta Tarayya, ba'a sauya dokokin ne matsalar take ba.

‘'Na farko dai wasu daga cikin wadannan batutuwa ni ina ganin magance shi ba wai lallai aikin tsarin mulki bane A'a. Kamar maganar cire garkuwa ko kariya ga shugaban kasa da mataimakinsa da gwamnonin da mataimakansu, alal- misali ko a tsarin da muke amfani da shi yanzu akwai tanaje-tanaje da dama da ya ba da damar in sun yi laifi za'a iya hukunta su. Amma kuma ba'a yi, kuma babu tabbacin cewa ko an yi gyaran . Haka nan hukumomin zabe na jihohi babbar matsalar ita ce gazawa ta zahiri ta su hukumomin da aka dorawa wannan aikin''.

Batun rike kudin kananan hukumomi da kuma zabe

Yunkurin rage tasirin da gwamnoni ke da shi a kan yadda ake tafiyar da kanana hukumomin Najeriya ta hanyar gyara dokar da za ta haramta asusun hadin guiwa tsakanin jihohi da kanana hukumin Najeriya dai batu ne da aka dade ana jiran ganin faruwarsa, musamman saboda yadda ake ganin gwamnonin jihohi sun rike wa kanana hukumomin wuya ta hanyar asusun hadin guiwa. Abinda Hon. Musa Sarkin Adar ya ce akwai abinda suka hango suke son ganin an koma tsarin da akae amfanai da shi a baya.

Treffen nigerianischer Gouverneure.
An zargin gwamnoni da rike kudaden kananan hukumomiHoto: DW

'Da kananan hukumomi suna samun kudaddensu kai tsaye da talaucin da ake fama da shi a cikin Najeriya da rashin aikin yin a matasa da kuma yadda ake almundahana da kudadden jama'a daga bangaren wasu gwamnonin Najeriya da hakan ba za ta faru ba. Shi shugaban karamar hukuma an zabe shine dai dai yadda aka zabi gwamna ko shugaban kasa, kuma an tanadar ma shi ya yi mulki a wannan karamar hukuma, don haka babu wani dalili da wani gwamnan ya zauna cewa duk kananan hukumominsa sai abinda yake so su yi za su yi''.

Kokarin yin kandagarki ga masu aikata laifuffukan zabe su tafi sakaka ya kama hanzar zuwa karshe, domin kwamitin majalisar na son ganin duk wanda ya aikata wadannan laifuffuka a hana shi tsayawa takara da za ta kai shi ga darewa kan duk wani mukamamin siyasa. To sai dai da sauran jan aiki kafin a kai ga samun wadannan sauye-sauye, domin a ranar talata ta makon gobe ne majalisar za ta fara muhawara a kan wadannan sassan da za ta sauya wa fasali a tsarin mulkin, kafin a kai batun ga majalisun jihohi.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe