Matsalolin boren adawa da gwamnati a Afirka | Siyasa | DW | 02.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalolin boren adawa da gwamnati a Afirka

Juyin juya hali da ƙasashen larabawa suka tsinci kansu a shekara ta 2011 ya bar ƙasashen Afirka cikin yanayi na zanga-zangar nuna adawa da gwamnatocinsu.

A taron Global Media Forum masu fafutuka daga ƙasashe huɗu na nahiyar sun yi nazari kan abin da ya rage shekaru uku bayan wannan rikici. Masu fafutuka da ke Addis Abeba fadar gwamnatin ƙasar Ethiopia na da wani salo na musamman da suke amfani da shi na gaisuwa kamar yadda marubucin Blog a ƙasar Eshete Bekele Tekle ya bayyana:

Ya ce "fitaccen gidan yari na da shiyyoyi takwas, shiyya na daya, biyu, uku, huɗu har zuwa takwas. Addis Abeba shi kansa shiyya na tara ne, wanda tamkar wani ɓangare ne na gidan yarin. Birnin ga baki ɗayansa gidan yari ne babu 'yancin walwala, saboda yadda gwamatin ke sa ido a kan ko wane abu".

Daga cikin mahalarta tattaunawar musayar ra'ayin dai har da ɗan jaridan ƙasar Chadi kuma mai fafutuka Eric Topona, wanda aka tsare a bara a Ƙasar dangane zargin kasancewar barazana ga tsarin mulkin Ƙasar.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da Usman Shehu Usman ya haɗa mana a kan kammala taron na GMF

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Abdourrahman Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin