Matsalar yunwa na addabar al′ummar duniya | Zamantakewa | DW | 02.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalar yunwa na addabar al'ummar duniya

A rahoton da ta bayyana a birnin Roma na Italiya hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya FAO ta ce kishi 12 cikin ɗari na al'ummar duniya ba su samin abinci mai gina jiki.

Za a iya cewar an sami raguwa ga lisafin da ake da shi a shekarun 2012 inda mutane kusan miliyan 868 suka yi fama da yunwar a shekarun 2010 zuwa 2012, yayin da a wannan shekara ta 2013 hukumar ta FAO ta addadin bai zarta miliyan 842. Yayin da mutun ɗaya bisa takwas ke fama da yunwa Amma duk da haka yawan masu fama da yuwan a duniyar ya ragu.

An ɗan sami ci gaba wajen yaƙi da yunwa a duniya

Fafatukar da ƙungiyar ta sha faman yi a tarrukan da aka gudanar na duniya daga shekaru 1990 zuwa 1996 shi ne na rage yawan al'ummar da ke fama da yunwar a duniya, kuma za a iya cewar ko da shike ma canji da aka samu bai taka kara ya kare ba, amma dai an ɗan sami ci gaba a yanki Asiya ta kudu maso gabashi inda a baya ake fama da kishi mai yawan na waɗanda ke fama da yunwa da kuma yankin Latin Amirka.

A kasashen yankin arewacin Afirka da na yankin Gabas ta Tsakiya lamarin yana da sauƙi ko da shike ma za a iya cewar wai dama-dama kibiya a ido. Josephe Schmidhuber shiB ne mataimakin darakatan hukumar abinci ta FAO.

Ya ce: ''A cikin ƙasashen na yankin arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya yaƙe-yaƙe na farar hula na daga cikin dalilan da suka taka muhimiyar rawa wajen asassa ƙarancin abinci, suna noma a binci a sa ɗaya kuma suna yin aikin hako ma'addinai a wuraran. Shi kansa wani cikas ne amma in' ba haka duniya na iya samar da abinci isasshe ga kowa har ma a yi saura.''

Ƙasashen Afirka ta yamma da na yankin gabashi a nan,lamarin ya fi yin ƙamari inda baya ga talauci al'umma suka sami kansu a cikin wani hali na rashin samin amfanin gona mai yawa abin da ya janyo yuwan.

Ƙasashen Afirka ta yamma sun fi fama da yunwar

Misali a cikin ƙasashen Guinee da Nijar da Senegal da Togo duk waɗannan ƙasaShe ne da suka taɓu yayin da ƙasashe irinsu Aljeriya lamarin ke da sauƙi. Simone Pott ɗaya daga cikin jami'an hukumar ta FAO ta ce babu sauyi a cikin sha'anin.

Ta ce: ''abubuwa ba su inganta ba don haka ba za mu iya maganar cewar ba an sami ci gaba, saboda kusan mutan ɗaya bisa biyar za su fuskanci matsalar ta yuwan a yankunan inda talauci da yuwan suka yi katutu dole sai mun tashi tsaye domin kauda wannan bala'i.''

Rahoton na hukumar ta FAO ya nuna cewar kishi 32 cikin ɗari na al'ummar da aka yiwa tamboyoyi na cewar yanayin rayuwarsu ya canza a cikin watannin 12 yayin da wasu 33 suka ce suna cikin wahala, kana kishi 34 suka ce babu wani sauyi da suka samu.

Mawallafi : Lüticke Marcus/Hassane
Edita : Umaru Aliyu