1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU za ta gina matsugunan 'yan gudun hijira

Lateefa Mustapha Ja'afarOctober 26, 2015

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta sha alwashin gina matsugunan 'yan gudun hijira 100,000 a kasashen yankin Balkan.

https://p.dw.com/p/1GuDr
Halin da 'yan gudun hijira ke ciki
Halin da 'yan gudun hijira ke cikiHoto: Reuters/L. Foeger

'Yan gudun hijirar dai na amfani da kan iyakokin kasashen na yankin Balkan wajen shiga kasashen da suka ci gaba a nahiyar Turai, hakan ce ma ta sanya yunkurin gina matsugunan a wani mataki na dakile matsalar kwararar 'yan gudun hijirar da kan iyakokin yankin gabashin Turai ke fuskanta. Shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ne ya sanar da hakan bayan da suka kammala wata tattaunawa ta gaggawa kan matsalar 'yan gudun hijirar a birnin Brussels. Shugabannin kasashe 10 na kungiyar Tarayyar Turan da suka hadar da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da kuma shugabannin kasashen da basa cikin kungiyar ta EU da suka hadar da Albaniya da Sabiya da kuma Macedonia ne suka gudanar da wannan taro na gaggawa a karshen mako biyo bayan gargadin da kaashen Bulgeriya da Romaniya da kuma Sabiya suka yi na rufe kan iyakokinsu da ke cunkushe da 'yan gudun hijirar da suke son tsallakawa kasashen da ke da karfin tattalin arzki a nahiyar ta Turai.