Matsalar ′yan ci-rani a ƙashen Larabawa | Labarai | DW | 10.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar 'yan ci-rani a ƙashen Larabawa

Hukumomin Saudiyya sun duaki matakan ba-sani ba-sabo kan baki da ke zama a kasarsu.

Foreign workers wait for a taxi as they leave the Manfuhah neighbourhood of the Saudi capital Riyadh on November 10, 2013, after two people have been killed in clashes between Saudi and other foreign residents the previous day, according to the Saudi police. On November 4, the authorities began rounding up thousands of illegal foreign workers following the expiry of a final amnesty for them to formalise their status. AFP PHOTO/FAYEZ NURELDINE (Photo credit should read FAYEZ NURELDINE/AFP/Getty Images)

'Yan ci-rani a Saudiyya

'Yan sanda a Saudiyya sun yi arangama da baƙi yan ci-rani a Riyad babban birnin ƙasar. 'Yan ci-ranin dai sun bada kai ne ga 'yan sanda, bayan mummunan tarzuma tsakaninsu da ya kai ga mutuwar muta ne. Dama tun daren jiya Asabar ne dai jami'an tsaro su ka yi wa baƙin zobe, a wani gidan da suka taru. A ziyar da ya kai birnin Makka wakilinmu Ado Abdullahi Hazzad, ya ji ta bakin wasu baƙin 'yan Najeriya da Nijar, inda wasu su ka soki rashin kulawa da baƙi na ofisoshin jakadancin ƙasashen. A fadar daya daga mutannen da ya zanta da su, ya sha zuwa ofishin jakadanci don a sake masa takardu, amma jami'an ba su taimaka masa ba. A yanzu haka dai 'yan sandan Saudiyya na loda mutanen cikin safa, zuwa wasu wuraren da aka kebe don tsare baƙin, kafin a mai da su ƙasashensu na asali.

Haka lamarin ya ke a Katar (Qatar)

Migrant labourers work on a construction site on October 3, 2013 in Doha in Qatar. Qatar, the 2022 World Cup host is under fire over claims of using forced labour. Global football's governing body FIFA kicked off a crunch meeting behind closed doors, amid claims of rights abuses by Qatar and wrangling over plans to hold the tournament in the winter. AFP PHOTO / AL-WATAN DOHA / KARIM JAAFAR == QATAR OUT = (Photo credit should read KARIM JAAFAR/AFP/Getty Images)

Ma'aikata baki da ke gina filayen kwallo a Katar

Babban jami'in MDD da ke kula da kare yancin dan Adam, ya buƙaci hukumomin ƙasar Katar da su, inganta yanayin dakunan kwanan baƙi 'yan ci-rani da ke ayyukan gine-gine a ƙasar. Jami'in wanda ya ganewa idanunsa inda baƙin ke kwana, ya ce wasu dakunan tamkar bukkoki ne. Akasarin baƙin dai na aikin gina filayen wasannin ƙwallon ƙafa da ƙasar ke shirin daukar nauyin gasar cin kofin a shekara ta 2022. Kungiyoyin kare yancin dan Adam, sun dade da kiraye-kiraye ga ƙasashen yankin Gulf, su inganta kula da yancin baƙi 'yan ci-rani. 'Yar mitsitsiyar daular Katar, ta yi mugun suna wajen rashin mutunta haƙin baƙi 'yan ci-rani.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu