Matsalar tsaro ta mamaye taron AU a Malabo | Labarai | DW | 26.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar tsaro ta mamaye taron AU a Malabo

Shugabar kungiyar AU ta ce kalubalen tsaro a wasu kasashen Afirka barazana ce ga nahiyar baki daya

Shugabar kungiyar Gamayyar Afirka ta AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta ce hare-haren ta'addancin da Najeriya da Somaliya da Kenya ke fuskanta a halin yanzu wata babbar barazana ce ga nahiyar Afirka baki daya.

Mrs Dalamini-Zuma ta ce magance hare-haren wani abu ne da ya kyautu kasashen Afirka su tashi tsaye wajen ganin an yi don gudun kada hakan ya dakushe bunkasar da nahiyar ke yi.

A sakonsa ga taron, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya shawarci shugabannin kasashen Afirka da su guji bai wa 'yan ta'adda damar cin karensu ba babbaka a kasashensu. Kana ya nemi shugabannin da su kaurace wa duk wani shiri na nuna wariya musamman ma ga masu neman jinsi guda.

Taron dai na kwanaki biyu wanda ke gudana a Equatorial Guinea na mai da hankalinsa ne kan batun noma da wadata nahiyar da abinci. sai dai ya zuwa yanzu hankali ya fi karkata ga batun samar da tsaro.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe