1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar tsaro ta jawo tsoro a Najeriya

Zainab MohammedMarch 4, 2013

Harbe kwamishinan 'yan sanda na jihar Kwara da aka yi ya jefa tsoro a zukatan 'yan Najeriya saboda kai wa ga mutanen da ke da cikakkiyar kariya da kashe kashe ba gaira suka yi.

https://p.dw.com/p/17qBs
Hoto: Katrin Gänsler

Karuwar hare-haren da ake samu a Najeriya kama daga na 'yan fashi da makamaki zuwa ga masu garkuwa da jama'a da ma uwa uba masu dauke da makamai a sassa daban daban na kasar, na zama abin damuwa da ma tambayar inda aka dosa a kan wannan mumunan hali da Najeriyar ta samu kanta a ciki, wanda a kullum masharahanta ke garagadin munin da ke da shi.

Polizeiposten in Millionenstadt Kano, Nordnigeria
Jami'an tsaro ma ba su tsira daga hare-hare ba a NajeriyaHoto: Katrin Gänsler

Kara sauyawar lamarin tsaro da ya zo sa'o'i 24 bayan gargadin da Janar TY Danjuna ya yi na cewar abubuwan da ke faruwa na nuna alamun kasar na fuskanatar barazanar yakin basasa ne. Na baya bayannan dai shi ne na kisan da aka yiwa kwamishin 'yan sanda na jihar Kwara Mr Chinwike Asadu a lokacin da ya kai ziyara a mahaifarasa da ke jihar Enugu, a yanayin da ya kara daga hankalin jama'a, saboda yadda aka yi wa motar da yake ciki ruwan harsasai duk kuwa da cewa mutum ne da ake ganin ya kamata yana da cikakken tsaro. Ga Malam Hussaini Mongunu masani a kan harkokin tsaron Najeriyar bayar da tabbacin cewa za'a iya shawo kan wannan matsala ya yi.

Hare-hare sun durkusar da tattalin arzikin arewacin Najeriya

Ko da yake gwamnati ta dade ta na ikirarain samun ci gaba a game da batun shawo kan matsalar ta rashin tsaro, amma tuni ta yi nisa wajen yin mumunar barna ga tattalin arzikin jihohi da dama da ke yakin arewacin kasar. Wannan ya sanya mutanen da dama nuna bukatar hanzarta daukan matakai na sadidan domin shawo kan matsalar da ta fara a matsayin dan hakin da aka raina. Abinda ya sanya Mr Max Benite masani a harakar tsaron Najeriyar bayyana cewa:

" gwamnati da 'yan sanda da sojoji kada su bari al'umma su dauke su a matsayin wadanda suka zo domin su samu nasara a kansu. Sai dai wadanda za su 'yantar da su daga matsalolin da suke fuskanta na kai masu hare-hare, to dole ne a samu canji domin samar da fata ga dan Adam shi ne babban al'amari idan babu fata ba dalilin wanzuwa."

Nigeria Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck ya ce ya na kokarin shawo kan matsalar tsaroHoto: AP

A yayin da ake Allah babi ya Allah a kan wannan matsala ba ga fararen hular Najeriyar da suke matukara neman kariya, su kan su jami'an tsaro ma ba su tsira daga hare-hare ba. Sukurkucewar da yanayin tsaron Najeriya ke ciki a yanzu ya yi matikar barnar musamman a fannin tattalin arziki da yanayin zamantakewar al'umma a daidai lokacin da harkokin siyasa ke kara zafafa.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mouhamadou Awal