Matsalar tsaro na yawaita a Tafkin Chadi | Siyasa | DW | 13.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar tsaro na yawaita a Tafkin Chadi

Tun bayan kifar da gwamnatin shugaban mulkin kama karyar kasar Libiya Mu'ammar Gaddafi kasashen Afirka musamman Afirka ta Yamma ke fama da matsalar tsaro.

Soldaten aus Niger bekämpfen Boko Haram (Getty Images/AFP/I. Sanogo)

Matsalar tsaro a yankin Tafkin Chadi

Kama daga Najeriya da makwabciyarta Jamhuriyar Nijar, sun fuskanci hare-haren ta'addanci cikin wannan makon, inda mutane da dama suka halaka. Sai dai duka kasashen biyu, na ikirarin cewa matsalar gtsaron ba ta rasa nasaba da rikicin kasar Libiya da ke makwabtaka, rikicin da ya rincabe tun bayan kifar da gwamnatin marigayi shugaban kasar ta Libiya Mu'ammar Gaddafi.

A 'yan kwanakin nan dai jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar, sun sanar da kane wasu gungun mutane dauke da makamai da suka ce daga Libiyan suke, kuma suna kan hanyarsu ne ta shiga Najeriyar. A yanzu dai duka kasashen biyu sun dukufa wajen lalubo hanyar kawo karshen matsalar tsaron, da ke hana al#umma sakat.

DW.COM