Matsalar satar mutane na kara muni a kasar Habasha
August 8, 2024Cikin makonnin da suka gabata ne aka yi tashin hankali a kasar Habasha, inda bayanai suka tabbatar da yin garkuwa da wasu daliban jami'a da ke cikin wasu motocin safa su akalla 160 wadanda ke hanyarsu ta zuwa hutu. Wasu mutane dauke da bindigoi ne dai suka tsare motocin guda uku a kusa da wani gari da aka kira Garba Guracha wanda ke a Tigray da lardin Oromia mai nisan kilomita 155 da Addis Ababa.
Daliban sun fito ne daga jami'ar Debark da ke yankin Amhara, inda aka wuce da su zuwa dazukan da aka yi amannar ‘yan tawayen yankin Oromo ke aikata aika-aikarsu. Kwanaki biyu bayan nan ne dai wasu iyalan suka ce suka soma samun kira daga dajin da masu garkuwar suke, ana kuma bukatar kudade na fansa, kamar yadda wata da aka sace wa ‘yaruwa ta bayyana wa DW ta wayar tarho.
Ta ce: "Na samu kiran waya daga ‘yar uwata a ranar hudu ga watan Yuli, bayan kwanaki biyu ba mu ji daga gare ta ba. Kiran ya yanke, ammam daga bisani su masu garkuwar da kansu suka kira inda suke bukatar da sai mu ba su dubu 500 na Birr kudin kasarmu. Kwatankwacin dala 6200 ko ma Euro 5700 kafin a sako mana ita."
Karin bayani:Matsalar yunwa sakamakon fari a Habasha
Wasu daga cikin iyalai sun tabbatar da samun kira daga masu garkuwar, inda aka bayyana musu kudaden da ko kusa ba za su iya hadawa domin ceto ‘ya'yansu da aka sace ba. Mako guda baya, wasu bayanai da suka fito daga gwamnatin yankin Oromia, sun sake birkita tunanin iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a Habasha.
Hukumomi sun ba da labarin samun nasarar ceto dalibai 160 daga cikin 167 da aka yi garkuwa da su a wani sintirin hadin gwiwa da al'umomin yankin. Sai dai ana kan ba da labarin ta kafafen yada labarai, wata ke cewa tana magana da ‘yar uwarta da ke hannun masu garkuwar a cikin daji.
Ta ce: " Yayin da nake sauraron jawabin gwamnatin a kan cewa an saki dalibai da suka kai 160, muke kan waya da ‘yar uwata da a yanzu haka ke hannun masu garkuwar. Kuna abin da take ce min shi ne akwai daliabi sama da 100 da suke hannun mutanen suna neman kudi na fansa. A gaskiya, mun ji kunya da abin da gwamnati ke fadi wanda ke kara baudar da mutane maimakon kawo musu sauki."
Karin bayani:Yankin Tigray na fama da matsananciyar 'yunwa
Iyalan daliban da ke hannu masu satar mutanen na kasar Habasha na cewa ba su sake samun wani bayani gamsasshe a kan halin da ‘ya'yansu ke ciki ba. Baya ga kasancewar dalibai cikin wadanda ke kan hadarin shiga hannun masu garkuwa domin neman fansa, su ma ma'aikata na kafmanoni da manima na shiga hannun bata-garin wadanda ke karuwa a kusan kullum a yanzu a kasar ta Habasha.