Matsalar rijistar masu zabe a Ghana | Siyasa | DW | 02.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar rijistar masu zabe a Ghana

Hukumar zaben kasar Ghana na kokarin ganin ta shawo kan matsalar rijistar masu kada kuri'a a zaben kasar da ke tafe.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama

Masu ruwa da tsaki da suka hadar da jam'iyyun siyasa da shugabannin addinai da kungiyoyin fararen hula da kuma 'yan jarida a kasar ta Ghana, sun dukufa wajen ganin sun gabatar da shawarwarin da ake bukata domin gudanar da kwaskwarima a kan batun yin rijistar zabe a kasar gabanin babban zaben shekarar 2016 da ke tafe. Hakan dai ya biyo bayan takaddama kan ko kasar ta Ghana na bukatar sake yin sabuwar rijistar kacokan, ko kuwa tsaftace tsarin yin rijistar shi ne abin da ya dace?

Zargin magudi a batun rijistar

Babbar jam'iyyar adawar kasar da ma wasu masu ruwa da tsaki dai, sun yi ta yin korafin cewar an sanya da sunayen baki kusan 75,000 da ma yara kanana cikin wadanda aka yi wa rijistar. An dai kafa wani kwamitin amintattu wanda suka yi alkawarin tsaida adalci a bisa shawarwarin da zasu gabatar ga hukumar zaben a yayin yin rajistartar masu zaben nan gaba. Shugaban kungiyar dake saka idanu a kan zabukan kasar ta Ghana CODEO a takaice, kana tsohon babban alkalin kasa kuma tsohon shugaban hukumar zaben kasar. V.C.R.A.C. Crabbe, shi ne ke jagoran wannan kwamiti, kuma ya ce:

"Akwai lokacin da shugaban hukumar zabe mai barin gado Dr Kodjo Afari Djan cikin bayaninsa ya ce tabbatar da sahihancin rajistar zabe nauyi ne da ya rataya a kan mu baki daya ba a kan hukuma kadai ba. A dalilin haka muna fatan kowane mai ruwa da tsaki a wannan batu zai yi cikin gaskiya, dan mu iya tan-tance hujjojin da aka gabatar acikin hikima kana mu gabatar da sakamakon mu na karshe ga hukumar zaben, wadda za ta yanke shawarar karshe da muke fatan za ta dore har zuwa al'ummar gaba."

Kalubalen da ke gaban hukumar zabe

Shugabar hukumar zaben kasar ta Ghana, Mrs charlotte Osei a nata bangaren ta ce, sun samu sama da wasiku 30 dauke da shawarwari da bukatun yin kwaskwarima a rijistar, a bisa wannan dalili ne hukumar bazata yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da ingancin rijistar zaben da kuma sahihancin zabukan shekarar 2016, ta kuma ce:

Shugaban jam'iyyar adawa ta NPP Nana Akufo-Addo

Shugaban jam'iyyar adawa ta NPP Nana Akufo-Addo

"Inganta rijistar zaben kasar musamman a yanzu da ya rage kasa da shekara guda a gudanar da zabukan gama gari na da muhimmancin gaske, a matsayin mu na hukuma mun saurari shawarwari daga kowane bangare kuma mun tan-tance, domin ginshikin ko waccee dimokradiyya shi ne jama'ar kasa, a dalilin haka samun hadin kansu shi ne matakin farko wajen tabbatar da ingancin zabuka da ma dorewan dimokradiyya. Zaman lafiya da tsaro, ci gaba da kare hakokin jama'a da ma tsayar da doka bazasu tabbata ba face da dimokradiyya."

Akasarin bangarorin da ke cece-kuce a kan wannan batu dai sun gabatar da shawarar amfani da katin rijistar 'yan kasa wajen raba wannan gardamar, ko shin hakan din zai dore? Irbad Ibrahim manazarci ne a kan al'amuran da suka shafi siyasa da tsaro da ma tattalin arziki ya kuma ce shawarar komawa ga rajistar 'yan kasa wajen yin wannan kwaskwarima na da sarkakiya, musamman a yanzu da ya rage kasa da shekara guda a kai ga babban zaben. Ya kara da cewa shi kansa katin 'yan kasar da aka fara bayar da shi tun a shekara ta 2010, har kawo yanzu ba'a kammala bayar da shi ba. A yayin da jam'iyyun adawa da suka hadar da NPP da PPP suke kan bakarsu na sake rijistar kacokan, ita kuwa jam'iyyar NDC da ke mulki da kuma jam'iyyun PNC da CPP da wasu kananan jam'iyyu masu zaman kansu, cewa suke wannan bukatar bata da makama.

Sauti da bidiyo akan labarin