Matsalar rashawa a fanin ilimi a Afirka | Siyasa | DW | 15.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar rashawa a fanin ilimi a Afirka

Kungiyar Transparency International da ke Afrika ta Yamma ta gudanar da wani taro a Abuja tare da kaddamar da binciken da ya gano mummunar matsalar cin hanci da rashawa a fannonin ilimi da mallakar filaye

Transparency International  matsalar da suka ce in ba'a dauki matakan gyara bat a yi nisa wajen lalata tsarin da jefa rayuwar alumma cikin mawuyaccin hali. Daga Abuja Uwaisu Abubakar Idris ya aiko da wannan rahoton.

Mahalarta wannan taro na kungiyar Transparency International daga kasashen Yammacin Afirka guda goma sun maida hankali ne a kan sakamakon binciken da ya girgiza kowa a kan ta'azzarar cin hanci da rashawa a fanin ilimi a kasashen guda biyar da suka hada da Najeriya, Liberiaya Jamhuriyar Niger da ma Ghana.

Domin baya ga wawashe kudadden da ake kasaftawa fanin ilimin, batun satar jarabawa da takardun boge na mumunar barazana ga daukacin tsari. A Najeriya koda a kwanan nan sai da aka yi dauki ba dadi a kan jarrabawar shiga jami'a da aka gano an tafka magudi.

Jamhuriyar Nijar dai na cikin kasashen da aka gudanar da wannan bincike inda suma anobar cin hanci da rashawa ta afkawa fanin ilimin kasar, musamman batun daliban boge da jabbun takardu.

Raoton ya gano cewa yadda lamari cin hanci ya yi muni a fanin ilimi, aka batun yake a fanin malakar filaye kama daga na noma da a muhalli da ke kara jefa alumma cikin kunci na talauci.

 

Sauti da bidiyo akan labarin