1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar makamai masu guba a Siriya

September 10, 2013

EU ta yi marhabin da yunkurin Rasha na warware cece-kuce a kan makamai masu guba a Siriya.

https://p.dw.com/p/19ffl
EU foreign affairs chief Catherine Ashton smiles at a press conference after the talks on Iran's nuclear programme in the Kazakh city of Almaty on February 27, 2013. Iran and world powers agreed today to hold new talks in March and April over the Islamic republic’s disputed nuclear drive, with Tehran hailing a 'more realistic' approach by their counterparts at two days of talks in Kazakhstan. AFP PHOTO / STANISLAV FILIPPOV (Photo credit should read STANISLAV FILIPPOV/AFP/Getty Images)
Hoto: Stanislav Filippov/AFP/Getty Images

Kantomar kula da manufofin ketare na Kungiyar Tarayyar Turai Catherin Ashton, ta bayyana yin marhabin lale da shawarar da kasar Rasha ta bayar, dangane da baiwa Majalisar Dinkin Duniya hurumin kulawa da makamai masu gubar da Siriya ta mallaka, domin lalatasu daga baya. Ashton, ta ambata cikin wata sanarwar da ta fitar cewar, tana goyon bayan wannan mataki, wanda ta ce kamata yayi sassan da abin ya shafa su yi aiki tukuru kuma cikin hanzari domin tsara daukacin bayanan da suka shafi hakan.

Dama ministan kula da harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, ya ce Rasha na yin aiki kafada-da- kafada da gwamnatin Siriya, domin tsara matakan aiwatar da shawarar da ta shafi makamai masu gubar, wanda kuma za su gabatar nan bada dadewa ba. Bayan hakane kuma, a cewar Lavrov zai kammala shirin, tare da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon da kuma Kungiyar Haramta Amfani da Makamai Masu Guba.

A martanin da ta mayar, Ashton, ta ce Kungiyar Tarayyar Turai mai kasashe wakilai 28, na goyon bayan wannan shawarar, da kuma aiwatar da ita yadda ya dace.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal