Matsalar fyade na kara ta′azzara a Najeriya | Zamantakewa | DW | 25.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalar fyade na kara ta'azzara a Najeriya

A Najeriya matsalar fyade na kara ta'azzara duk da matakan da hukumomi ke ikirarin dauka domin tunkarar matsalar. A kan haka ne kungiyoyin kare hakkin mata da yara suka kara matsa kaimi a kokowar da suke.

Sannu a hankali matsalar fyade na ci gaba da yaduwa a Tarayyar Najeriya inda kusan a kowace rana ta Allah akan bankado mutanen da ke yi wa matan aure da 'yan mata cikin har da yara kanana da ma jarirrai da ma kanan yara maza fayde.

 

A baya bayan nan 'yan sanda sun yi nasara kama wani matashi da ya yi ikirarin yi wa mata sama da 40 fyade a cikin gidajensu. Labari mafi muni ma dai shi ne na wani mutum da ya yi wa wata jaririya 'yar watanni uku fyade a Adamawa inda har ta kai hanjin cikinta ya fito waje. Ta kai dai sai da aka yi wa jaririyar aikin tiyata wajen 12. A kan haka ne ma a baya bayan nan kungiyoyin kare hakkin mata da yara suka matsa kaimi wajen ganin mahukuntan sun tsaurara dokokin hukunta masu aikata fyade.

A wasu yankunan ma kamar Jihar Bornon masu fafutikar sun gudanar da zanga-zanga. Kazalika malaman daga addinai dabam-dabam a Tarayyar ta Najeriya sun nuna takaicinsu dangane da yadda wannan matsala ta fyade ke kara kamari, tare kuma da bayyana ra'ayoyinsu kan dalilin gurbacewar al'umma da kuma irin matakan da addinan suka tanada domin tunkarar irin wannan matsala idan ta bayyana a cikn al'umma.Matsalar ta fyade a Tarayyar ta Najeriya na kara kamari ne duk da ikirarin da mahukuntan kasar ke yi na daukar matakai a kai.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin