Matsalar fashi da makami a Ghana | Siyasa | DW | 01.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar fashi da makami a Ghana

Kasa da sa'o'i 24 kasar Ghana ta fuskanci barazanar 'yan fashi da makamai musamman a Accra babban birnin kasar da kuma Tema, hakan ne ya sanya hukumomi daukan kwararan matakai na tsaro.

Guraben da aka aiwatar da wadannan miyagun ayyukan sun shafi inda ake aikawa da kudade ta wayar cellula wato Mobile Money, bankuna tare da shagunan da ake canjin kudade na kasashen ketare. Hakan dai ya sa jama'a bayyana fargabansu tare da cewa ya kamata shugaban 'yan sandan kasar ya yi murabus ganin yadda ake ganin kasawarsu wajen samar da tsaro a manyan biranen kasar. Sai dai kuma wasu na ganin cewa bai kamata shugaban 'yan sandan ya yi murabus ba. Da yammacin wannan rana ta Alhamis ce, ministan yada labaran kasar ta Ghana, ya kira wani taron manema labarai, inda ya gabatar da matakan gagauwa da gwamnati ta dauka tare da shugabanin tsaro na kasa baki daya. 

Jami'an tsaro masu kwantar da tarzoma a Ghana

Ministan ya fara ne da cewar daga yanzu a tabattar cewar zasu rinka ganin 'yan sanda tare da sojoji a unguwanin da aka fi aiwatar da wadannan miyagun ayyukan, wato "operation calm life" kenan,  kuma wajibi ne dukkanin bankuna da ma makamantansu su fara amfani da CCTV Camera wanda za a kafa cibiya ta musamman inda dukkanin abinda ke faruwa a ko'ina za su gani tare da tabattar da  cewar an farfado da fitillu a manyan tituna kasar baki daya.  Sannan a karshe ministan ya sanar cewa 'yan sanda kadai ne za su yi amfani da siren/ busa da jami'an tsaro ke sakawa a motocinsu, kuma duk wani farar hula da aka kama ya keta wannan dokar, zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Ana iya cewa dai ma'aikatar tsaron kasar ta Ghana ta kama hanyar saka kafar wando daya da 'yan fashi da makami da suka bullo da sabin dubarun sata a cikin kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin