Matsalar cin zarafin mata a Amirka ta karu | Labarai | DW | 01.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar cin zarafin mata a Amirka ta karu

Sojoji da ke yi wa mata fyade da makamacin haka a wuraren aikinsu, a yanzu ya kai kashi 50 cikin dari, abinda kuma ke nuna ya karu matuka fiye da tunanin hukumomi

Wata sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta Amirka wato Pentagon ta fitar, ya nuna yadda alkaluman irin kararakki da ake samu na cin zarafin mata a wuraren aiki ke karuwa. A cewar Pentagon, duk da irin kokarin da hukumomi ke yi na magance lamarin, amma kuma sai karuwa yake yi. Rahoton yace a shekaru biyu da suka gabata, an samu karakin cin zarafin mata kimanin 3,374. Amma kuma a bara alkaluman sun karu da kashi 13, abinda kuma ya sa yanzu yawan matsalar cin zarafin ta kai kashi 50 cikin dari. Lamarin da kuma hukumomi suka ce na tada hankali ne.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Naisru Awal