Matsalar baƙin haure masu zuwa Turai | Labarai | DW | 02.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar baƙin haure masu zuwa Turai

Wani kwale-kwale ɗauke da baƙin haure daga Afirka ya yi hatsari a tekun Baharamaliya kusa da gaɓar ruwan Italiya

Rundunar sojan ruwan ƙasar Italiya suna kan ceto mutane 233, da ke cikin wani kwale-kwale, a kan hanyarsu ta shiga Italiya bisa ɓarauniyar hanya. Rahotanni suka ce wani jirgin helikoptan ƙasar Italiya ne ya haggo kwale-kwalen a cikin daren jiya. Akasarin baƙin haure da ke ciki, 'yan asalin ƙasashen Najeriya, Eriteriya, Somaliya, Pakistan, Zambuiya da Mali ne. Ganin yawan mutane da ke maƙare cikin kwale-kwale, ya sa sojan ruwan Italiya ƙaddamar da aikin na dokar ta-ɓaci don kawo ceto cikin gaggawa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu