Matsalar baƙin haure daga Afirka zuwa Turai | Labarai | DW | 21.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matsalar baƙin haure daga Afirka zuwa Turai

Wasu baƙin haure ɗauke da makamai sun gobza da jami'an tsaron ƙasar Spain, bayan da suka nemi shiga ƙasar ta ɓarauniyyar hanya

Ein Boot der spanischen Küstenwache bringt afrikanische Füchtlinge nach Fuerteventura; die Küstenwache hatte sie auf einem heruntergekommenen Boot, dessen Wrack (l) sie im Schlepp hat, auf dem Meer vor den Kanarischen Inseln abgefangen (Archivfoto vom 19.10.2004). Viele der Migranten sind eigentlich wohlhabende Menschen, eine Reise nach Europa kann bis zu 10.000 Dollar kosten. Doch die Chancen, den gelobten Kontinent zu erreichen, werden immer geringer. Von Afrika aus führen viele Routen nach Europa, Ceuta und Melilla sind nur eine der möglichen Zwischenstationen. Foto: Juan Medina (zu dpa 0617) +++(c) dpa - Bildfunk+++ Afrika, Gesellschaft, Migration, Politik

Baƙin haure daga Afirka ke cikin zuwa Turai

A ƙasar Spain aƙalla yan sanda shida suka jikkata, bayan arangama da suka yi da baƙin haure dake neman shigowar ƙasar. Baƙin hauren da suke ɗauke da sanduna da wuƙaƙe, sun gobza da 'yan sadan ne bayan da aka nemi hanu su shiga ƙasar ta Spain, yayinda suka fito daga ƙasar Moroko cikin kwale-kwale. 'Yan sanda sun tsare biyar daga baƙin hauren, amma sauran sun sulale sun shiga ƙasar ta wani tsibiri dake yankin Afirka. Aƙalla baƙin haure 80.000 suke zama a tsibirin Melilla inda lamarin ya faru. Dubban yan gudun hijira ne dai daga ƙasashen Afirka, ke neman shigowa Turai ta ɓarauniyar hanya, don neman rayuwa mai inganci, inda da damansu kan rasa rayuka bisa hatsarin da hanyar ke da shi.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Mohammed Abubakar