Matsalar baƙin haure a cikin ƙasashen Turai | Siyasa | DW | 08.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar baƙin haure a cikin ƙasashen Turai

Baƙin haure da kuma 'yan gudun hijira da ke ƙoƙarin shigowa Turai ta ko wacce kafa, sun addabi ƙasashen nahiyar .

Ministocin harkokin cikin gida na ƙungiyar Tarayyar Turai, sun gana domin tattauna matsalolin baƙin haure daga nahiyar Afirka da Gabas ta Tsakiya da ke yin tururuwa domin shigowa Turai ta ko wacce hanya, musamman ma ta ruwa wanda hakan ke haddasa asarar rayuka a wasu lokutan.

Taron da ministocin ƙungiyar Tarayyar Turan suka gudanar, a shalkwatar ƙungiyar da ke Brussels babban birnin ƙasar Belgium, ya tattauna batun ƙara samar da kayan aiki da kuma kara faɗaɗa sintiri a gabar tekun Mediterranean, domin magance samun yawaitar kwararowar baƙin haure da suke ƙoƙarin shiga ƙasashen Turan.

Da ta ke jawabi a yayin taron, kwamishiniyar lura da harkokin cikin gida ta ƙungiyar Tarayyar Turai, Uwargida Cecilia Malmstroem, cewa tayi za ta yi ƙokarin ganin an faɗaɗa sintiri da kuma ayyukan ceto a yankin gabar tekun da mafiya yawan baƙin haure ke amfani da shi wajen shigowa Turai.

Kasashen nahiyar Turai na kokarin magance matsalar bakin haure

Ta kara da cewa za ta yi ƙokarin ganin ta samu goyon baya, domin samar da ƙarin kuɗaɗe da kuma kayan aiki da za'a faɗaɗa ayyukan sintiri daga Tsibirin Cyprus zuwa ƙasar Spain, domin rage asarar rayukan da ake yi a yankin.

Italien Flüchtlingsdrama Lampedusa

Wasu daga cikin gawawwakin da aka samu, bayan hadarin jirgin ruwa a Tsibirin Lampedusa na Italiya.

Haka kuma ta amince da cewa ya kamata a samu dai-daito wajen rarraba ɗaukar nauyin 'yan gudun hijira da kuma bakin haure da suke zuwa Turai, tana mai cewa daga cikin ƙasashe 28 da ke cikin ƙungiyar ta Tarayyar Turai, ƙasashe shida zuwa bakwai ne kawai ke ɗaukar nauyin 'yan gudun hijirar da ma bakin haure.

A nasa jawabin ministan harkokin cikin gida na nan Jamus Hans-Peter Friedrich, ya buƙaci hadin kan shugabannin ƙasashen Afirka ne domin shawo kan matsalar.

Ya ce: "Muna buƙatar hadin kan shugabannin ƙasashen Afirka domin shawo kan wannan matsalar ta baƙin haure, Wannan wani babban abin takaici ne".

Minista Hans ya kuma ƙara da cewa, Jamus ita ce ƙasar da tafi ba da mafaka ga baƙin haure da kuma 'yan gudun hijira a nahiyar Turai baki ɗaya.

Italian Financial police scuba divers prepare their gear at the Lampedusa island, Italy, Sunday, Oct. 6, 2013. Authorities say divers have recovered new bodies from a fiery shipwreck of a fishing boat packed with 500 migrants from Eritrea. Financial police Maj. Leonardo Ricci said divers have recovered about 10 bodies since resuming the search Sunday morning. He said the search and recovery would continue as long as the sea is calm and there is light. (AP Photo/Luca Bruno)

Ma'aikatan ceto na ci gaba da lalubo sauran gawawwakin da ba a gano ba, a hadarin jirgin ruwan da ya afku a Tsibirin Lampedusa

A shekarar da ta gabata dai kaso 70 cikin 100 na 'yan gudun hijira kimanin dubu 330, da suka shigo Turai an raba su ne zuwa ƙasashen nahiyar Turan biyar, inda Jamus ta ɗauki nauyin kimanin 'yan gudun hijira dubu 77 da 500 yayin da Faransa ta ɗauki nauyin dubu 60 da 600 ita kuwa Sweden ta ɗauki nauyin dubu 44. Su kuwa ƙasashen Birtaniya da Beljium sun ɗauki nauyin 'yan gudun hijira dubu 28 ne kawai kowannensu.

Bukatar samun dai-daito wajen daukar nauyin 'yan gudun hijira

A nata bagaren, shugabar hukumar dake kula da Tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, Giusi Nicolonini, da a yanzu haka yankin bai gama farfadowa daga razanar da ya tsinci kansa a ciki ba, a sanadiyyar hadarin da wani jirgin ruwan fasinja mai dauke da bakin haure sama da 500 ya yi a yankin, ta bukaci da a yi gyara a kan yarjejeniyar Dublin ta 2.

Ta ce: " Ina son ƙungiyar Tarayyar Turai wato EU, ta yi gyara kan yarjejeniyar Dublin ta 2, waddada ta ce duk ƙasar da baƙin haure suka fara isa ita ce za ta ɗauki nauyinsu, ya kamata ko wace ƙasa da ke nahiyar Turai ta ɗauki rabonta".

Matsalar baƙin haure da kuma 'yan gudun hijira dai yanzu ita ce abin da ke ciwa ƙasashen nahiyar Turai tuwo a kwarya, domin kuwa ko da sanyin safiyar Talatar nan sai da aka ceto kimanin bakin haure 400, da ake kyautata zaton sun fito daga ƙasashen Siriya da Palasɗinu, yayin da jirgin ruwan da suke ciki ya shiga cikin haɗari a gabar tekun ƙasar Italiya, a ƙoƙarin da suke na shigowa Turai.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin