Matsalar ƙwayar cutar HIV a Tanzaniya | Zamantakewa | DW | 31.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Matsalar ƙwayar cutar HIV a Tanzaniya

Mutane milliyan ɗaya da ɗigo shidda ke ɗauke da ƙwayar cutar HIV, kusan kashi shidda ke nan cikin 100 na mutane milliyan 41 da ke ƙasar.

Asusun nan na Global Fund to Fight AIDS da ke yaki da cutar nan da ke karya garkuwar jiki ta AIDS ko SIDA ya ce kasar Tanzaniya ta yi namijin kokari wajen cigaba da ta samu a yakar cutar da ma dai cutuka irinsu tarin fuka da Malaria wanda dukanninsu ke saurin hallaka mutane.

Wannan cigaban da Tanzaniya ta samu da ba zai rasa nasaba da yunkurin da aka yi wajen samar da magani na cutar ta AIDS ko SIDA ba musamman ma dai daga farko shekarun 1990 lokain da yawan da wadanda ke dauke da wannan cuta ya yi kasa da kusan kashi shidda cikin dari.

Baya ga batun samar da magunguna da kula da masu dauke da wannan cutar, a hannu guda mahukuntan kasar sun tashi haikan wajen wayar da kan mutane don ganin sun kare kansu daga kamuwa da cutar da ma yin gwaji don sanin matsayinsu.

Kowa na magana kan ƙwayar cutar HIV

Wannan yunkuri ne ma ya sanya Dr. Christoph Benn da ya taba aiki a guda daga cikin asibitocin da ke Tanzaniya kuma yanzu haka babban jami'i a asusun yakar cutar AIDS na Global Fund to Fight AIDS ya ke ganin ya dakushe kaifin kamu da cutar domin mutane sun fahimci cewar daukar cutar ba wai ya na nufin karshen rayuwar mutum ba kenan.

Da ya ke tsokaci kan batun na wayar da kai, Dr. Sulaiman Muttani na asibitin Temeke da kasar ta Tanzaniya ya ce shakka babu hakan ya sanya samun gagarumin cigaba a yakin da ake da cutar ta AIDS.

"Yanzu haka zan iya cewa ana samun sauki saboda mutanenmu na kara ilimantuwa cewar cuta ce da za a iya rayuwa da ita ba tare da ta kashe mutum nan take ba saboda za a iya shan magani kuma yanzu muna kokarin wayar da kan mutane cewar cutar ta fi saukin kulawa da ita fiye da ciwon sukari ko Diabetes".

Tuni da wannan batu na wayar da kai ya shiga jikin mutane da sauran masu dauke da cutar musamman ma idan ana batu na nun kyama ga masu dauke da ita wanda ke taimakwa wajen hallaka su. JapoHemedi wani mai dauke da cutar ne ya kuma yi mana karin haske game da batun na rashin nuna kyama.

Ana iya rayuwa da ƙwayar cutar HIV

Ban taba fuskantar nuna wariya ko kyama ba saboda ina dauke da wannan cuta. Lokacin da na gayawa iyalina da sauran 'yan uwana cewar ina dauke da cutar basu kyamace ni ba, sun rungumeni hannu bibiyu. haka ma abin ya ke ga makota, don haka sai na cigaba da karbar magunguna wanda ya sa yanzu haka na ke cikin kyakkyawan yanayi.

Wani abu har wa yau da ya sanya samun cigaba a Tanzaniya game da yakar wannan cuta shi ne yunkurin da kungiyoyin kasa da kasa da gwamnatin Tanzaniya ke yi na ganin sun magance yaduwar cutar daga uwar da ke dauke da ita zuwa dan da za ta haifa.

Baya ga wannan batun rabon kwaroron roba am dai wani jigo ne na wannan fafutukura da yaki da cutar ta AIDS da ma dai bunkasar tattalin arziki da kasar ta samu a dan tsakanin nan wanda yanzu haka ya sanya gwamnatin kasar sanya kudi masu dumbin yawa a harkoki na kiwon lafiya.

Mawallafi: Gehrke, Mirjam/Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal