Matsa lamba kan Merkel game da batun leken asiri | Siyasa | DW | 15.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsa lamba kan Merkel game da batun leken asiri

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel tace za ta matsa lamba domin ganin an kare bayanan kasashen kungiyar hadin kan Turai a aiyukan hukumar leken asiri ta NSA.

Angela Merkel ta kuma yi alkawarin matsa lamba ga kamfanoni na Intanet a game da kiyaye dokokin Jamus da na Kungiyar Hadin Kan Turai game da tatsar labarai da bayanan sirri na jama'a, saboda da dalilai na tsaro. Shugaban gwamnatin tayi bayanin haka ne a yunkurin kwantar da zukatan jama'a dake nuna rashin jin ddinsu sakamakon rahotannin cewar hukumar leken asirin Amirka ta NSA ta na amfani da hanyoyi na haramun domin tara labaran sirri na jama'a a Jamus da sauran kasashen Turai.

Lokacin hira da tashar telbijin ta ARD a nan Jamus, shugaban gwamnati Angela Merkel ta kare hadin kan dake akwai tsakanin hukumar leken asirin Amirka da takwarar ta ta Jamus, inda kuma tace ba daidai bane a rika kwatanta aiyukan hukumar leken asiri ta NSA ta Amirkaq, da tsohuwar hukumar leken asirin Jamus ta gabas wato hukumar Stasi. Duk da haka, Merkel tace tana sa ran samun hadin kai da hukumomin leken asirin Amirka da na Jamus, a kokarin warware sabanin dake tsakanin bangarorn biyu, kan rahotannin tara bayanan sirri na jama'a, musamman na kungiyar hadin kan Turai ba tare da sanin wadanda abin ya shafa ba. Tace tana kuma sa ran nan gaba, Amirka zata kiyaye dokokin da Jamus ta shimfida a game da tara bayanai da kare sirrin jama'a a kasar.

USA Screenshot Website der NSA

Shafin Intanet na hukumar leken asirin Amirka NSA

Tace al'amarin dake da muhimmanci a gareni shine: shin hukumomin leken asirin na Amirka dake aiyukansu a nan Jamus, suna kiyaye sharudda da dokokin da Jamus ta shimfida a game da tara labarai da bayanan sirrin na yan kasa? Wannan dai shine bukatarmu. Za'a kuma yi bincike a game da haka, a ga ko Amirkawan a da can sun kiyaye dokokinmu ko basu kiyayesu ba. Dangane da haka, shugaba Barack Obama ya bada umurnin a cire kariyar tsaro a wasu jerin kundayen takardu na bayanan da Amirkan ta tatsa, yayin da kwararrunmu zasu ci gaba da shawarwari da Amirkawan, kuma ina sa ran samun alkawari mai karfi daga Amirka dake tabbatar mana da cewar nan gaba zasu rika kiyaye dokokinmu yayin da suke aiki a kasarmu. Dukanmu dai kawayen juna ne kuma mun kasance a kungiya daya ta tsaro, saboda haka wajibi ne mu rika mutunta bukatun juna.

Shugaban gwamnatin ta Jamus tace ya zuwa yanzu, bata da wani bayani dake nuna cewar hukumomin leken asirin na Amirka basa kiyaye dokokin Jamus a aiyukan su ba a nan Jamus. Wannan al'amari ne da kwararru zasu yi nazari kansa kuma bayan bincike su gabatar da rahoto ga majalisar dokoki. A game da rahotannin dake cewar hukumar NSA ta Amirka tana ma sauraron abin dake gudana a fadar ita kanta shugaban gwamnatin da kuma tara bayanai ba bisa ka'ida ba, Angela Merkel ta nunar da cewar:

Edward Snowden

Tsohon ma'aikacin hukumar leken asiri ta NSA, Edward Snowden

Muna nan muna ci gaba da bincike, amma ni kaina bani da labarin cewar hakan ya faru ko yana faruwa. Saboda haka ne kwararrunmu suke tattaunawa da takwarorinsu na Amirka. Ina kuma ganin umurnin da shugaba Barack Obama ya bayar na cire kariyar tsaro kan wasu takardu na bayanan sirrin wadanda ya zuwa yanzu muka kasa taba su, domin sanin gaskiyar halin da ake ciki, wani al'amari ne da zai bamu kwarin gwiwa. Ni kaina bani da labarin wani wuri ko lokacin da aka saurari abin da nake yi a asirce. Domin inda na sani, da na gabatar da rahoto ga kwamitin aiyukan leken asiri na majalisar dokoki.

Wannan abin kunya na aiyukan leken asirin Amirka a Jamus, yana neman zama kan gaba a jerin al'amuran da za'a maida hankali kansu a kampe na neman kui'un jama'a a zaben majalisar dokoki mai zuwa cikin watan Satumba, inda yan adawa suke zargin shugaban gwamnatin da yiwa wannan al'amari mai muhikmanci da ya shafi sirrin yan kasa shakulatin bangaro.