A Najeriya wata matashiya a jihar Gombe da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar, na amfani da shara domin samar da makamashi da kayan adon gida da daki. Matashiyar dai kan yi amfani da takaddu da robobin ruwa da makamantansu, domin sake sarrafa su zuwa wani abin amfanin na daban.