1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HdM: Matashiya mai sayar da shayi

May 20, 2020

Sana'ar sayar da shayi, sana'a ce da aka fi sanin maza da ita a Najeriya, sai dai a jihar Adamawa wata matashiya ta rungumi sana'ar.

https://p.dw.com/p/3cWOm
Nigeria Adamawa Tee-Verkäuferin
Justina John mai sana'ar shayi a Adamawa

Wannan matashiya mai suna Justina John ta zabi ta nemi sana'ar dogaro da kanta ba sai ta yi aikin gwamnati ba. Matshiyar dai ta nunar da cewa ta cimma nasarori cikin wannan sana'a tata, koda yake ba a rasa kalubale. Ta kuma bukaci matasa da su tashi su nemi na kansu, tana mai jaddad muhimancin yin sana'ar hannu.