Matashin mai nakasa a Malawi ya tashi tsaye | Himma dai Matasa | DW | 13.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashin mai nakasa a Malawi ya tashi tsaye

Matashin mai nakasa a Malawi ya tashi tsaye wajen samar da sana'oi ga mutanen da yake rayuwa inda ya zama abin misali.

Wani mai nakasa a kasar Malawi mai suna Masautso Chikutse, wanda duk da cewa ya taso daga yanki na ‘yan rabbana ka wadatamu, amma kuma ya yi ta gwagwarmaya har ya kai ga kirkiro da tsare-tsaren da ke taimaka mutanensa. Shi dai Masautso Chikutse an haifeshi ne a shekara ta 1977, kuma lokacin da ya taso yana tunanin cewa ba zai iya kullo komai ko dan karan kanshi ba. A kullun dai yana dogaro ne da wasu wajen samun taimako. Babbar matsalar dai ya fuskance ne a shekara ta 2003 inda ta kais hi ga rashin mafita illa ya shiga yin bara bisa titi domin ya samu wani abun kula da matarsa da kuma ‘ya'yansa.

Bayan da aka yi ta kaskantar das hi na tsawon lokaci sakamakon wannan bara da yake yi, Chikutse wanda yake mahaifi na ‘ya'ya biyu, ya kudiri a niyyar dakatar da wannan aiki na bara day a sa wa gaba, tare da yi wa kan shi karatun ta nutsu na ganin ya canza dubara domin ya samu mai fitar das hi daga wannan kangi day a samu kan shi a ciki. Ta haka ne ta ‘yan kudadan day a tara na bara, ya sayi na'urar daukan hoto ta zamani.

Sai dai kuma kash, ita ma wannan sana'a ta hoto da Masautso Chikutse ya runguma ba ta samar masa da kudadan da ya yi tsammanin samu. Hakan ta say a yi watsi da wannan sana'a, inda ya kudiri a niyar yin tallar kayayaki. To a wannan lokaci ne  Chikutse ya kai kanshi inda wata kungiya da ake cewa  Mpita Comsip wadda ta ke a matsayin asusun ajiyya da kuma zuba hannun jari, har kuma ya samu zama memba ga wannan kungiya.

A yanzu haka dai Masautso Chikutse ya kasance wakilin kamfanin wayar sadarwa na Airtel a garinsu, yana da shago, har ma yana bayar da bashi na kukade ga mutane,  Rozina Tafatatha ita ma memba ce ga wannan kungiya da Chikutse ya shiga ta asusun ajiya da  zuba hannun jari, cewa ta yi da dama daga cikinsu sun samu gina gida na zamani, sannan sun samu damar biya wa ‘ya'yan su kudadan makaranta ta hanyar tallafin da suke samu daga kungiyar.

Baya ma ga kaddarori da ya mallaka a yanzu haka, kudin da Chikutse ya mallaka ya kai kimanin miliyan shida, inda kuma ya karkata a kan harkokin kiwo na dabobi.