Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Idris Bilyaminu Ndasadu'Lau da ke karatu a fannin kimiyyar halicce-haliccen duniya a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, yana dinka audugar mata domin raba wa marasa galihu a kyauta, tare da koya wa wasu mata yadda ake dinka ta.
Wata kungiyar 'yan ta'adda ta karbe iko da wasu sassan yankin birnin Gwari na jihar Kaduna a arewacin Najeriya, inda ta haramta jama'a gudanar da duk wasu taruka na siyasa.
Wani matashi a jihar Kano da ke Tarayyar Najeriya, ya rungumi sana'ar harhada turare na Afirka da ma na Larabawa.
A kokarin janye samari matasa guragu daga barace-barace a kan hanya dan kama sana'ar yi, wani matashi nakasasshe ininiya a garin Kaduna na Najeriya ya horas da matasa nakasassu sana'ar walda.
Matashin Musa Muhammad ya kware wajen aikin kere-kere wanda ta hanyarsa wasu matasan kan samun horo domin yin dogaro da kai.