Matashi mai wakar Gambara ta zamani | Himma dai Matasa | DW | 28.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matashi mai wakar Gambara ta zamani

Wani matashi mai wakar Gambara ta zamani ya fito da tsarin kawar da talauci ta hanyar wakoki da suke karfafa wa matasa gwiwa akan dogaro da kai.

Masa'ud Abubakar Yarima yace matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa musamman mazauna birane na ci gaba da kuntatawa iyalai. Yana fatan wakokinsa su taba zukatan matasa ta hanyar rungumar sana'o'i.

Duk da irin wannan kalubale Yarima ya fuskanta ya sha alwashin ci gaba da rera wakoki na zamani masu dauke da sako ga matasa da kuma nishadantarwa domin a fahimtarsa idan ba a sauya tunanin matasa akan sana'a ba to ko nawa aka basu a matsayin jari ba za su yi tasiri ba

Sauti da bidiyo akan labarin