Matasan Nijer sun yunkara a siyasar kasar | Siyasa | DW | 17.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matasan Nijer sun yunkara a siyasar kasar

A kokarin kwato 'yancin gashin kansu daga hannun 'yan siyasar Nijer wasu kungiyoyin matasa a kasar ne suka kafa wata kungiya mai shirin tsayar da matasa a matsayin 'yan takara masu zaman kansu.

Niger Niamey Proteste AREVA Uran

Matasa sun fito gangami a Niger

Kungiyar mai suna Révolution Populaire Pour le Changement CPR a takaice na mai shirin shiga ka'in da na'in cikin gwagwarmayar tabbatar da matasan kasar su cimma gacci tare da kai su a wani matsayin koli da ke tilastawa hukumomi damawa da su wajan tafiyar da mulki, ta hanyar shiga takara a matsayin 'yan takara masu zaman kansu a zabubbukan da kasar ta Nijer ke shirin shiryawa a 'yan watanni kalilan.

Tun da jimawa dai matasan kasar Nijer da su ne mafiya yawa daga cikin al'ummar kasar suka sha kokawa da rashin kulawar wadanda suka kira gajiyayyu a fagen siyasa da kuma suka jima suna ci da guminsu, hasali ma tsoffin 'yan siyasar sun mayar da matasan tamkar wasu karnukan farauta wadanda idan aka samu mulki sai a barsu da kura kurum.

Malam Muhammad El kabir na daya daga cikin shuwagabannin kungiyar matasan kuma ya bayyana mana manufofinsu.

" Manufar ita ce don zaben nan da ke tafe na 2016, matasa su kori duk wadan nan tsaffin 'yan siyasar, saboda haka munka kirkiri wannan kungiya saboda matsalolin matasa. Idan har ba matasa suka tashi tsaye ba suka yi canji ba to ba mafita. Hanya kuwa ta kawo canji shi ne ta hanyar shiga siyasa mu kawo sauyi a shekarar 2016".

Niger Wahlen Politik Stimmen Auszählung

Jami'an zabe a Niger

Tuni dai kungiyar ta ke ci gaba da samun yabo da guda daga wasu matasan kasar da ke ganin lokaci ya yi na sauyi.

Ko baya ga wannan gwagwarmayar wasu kungiyoyin matasa ire iren su AJDDN mai jagorancin Malam Habila Rabiou na mai ganin da sauran aiki mai mahimmancin gaske a gaba.

"Zamu yi kokari a matsayinmu na kungiyoyin matasa mu hada kai mu tilasta wa 'yan majalisunmu su sanya doka ta cewar kamar yadda aka sanya dokokin cikin kundin tsarin mulki da kundin zabe da na tafiyar jam'iyyun siyasa da suka tilasta wa hukumomi da jam'iyyun siyasa wani kaso na siyasa, saboda hakan zamu tilasta wa 'yan majalisunmu da su kafa irin wannan dokar ga su ma matasa cewar a tilastawa jam'iyyu da su sa kaso kaza na matasa da za'a karbi takardun takararsu".

Allah ya albarkaci jamhuriyar Nijer da dimbin matasa masu yawan gaske da ke kiran kansu ko da yaushe manyan gobe sai dai fatara da talauci da rashin aikin yi na kasancewa wata babbar barazana ga matasan, abubuwan da matasan suke cewar laifi ne da ya fito daga 'yan siyasa saboda rashin cika masu alkawuran da suke dauka tun daga lokacin da suke cikin yakin neman zabe.

Sauti da bidiyo akan labarin