Matasan Najeriya sun yi zanga-zangar neman daman shugabanci | Siyasa | DW | 25.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matasan Najeriya sun yi zanga-zangar neman daman shugabanci

Tattakin na bukatar rage yawan shekaru na izinin shiga takara a siyasar Najeriya, wannan tattakin ya zo ne a dai-dai lokacin da majalisar ke shirin fara jefa kuri’ar amince wa da sauye-sauyen kundin tsarin mulki.

Nigeria - Jugenddemonstration not too young in Abuja (Uwais Abubakar Idris)

Dandazon matasan Najeriya maza da mata a yayin zanga-zangar

Dubban matasa ne dai suka fito duk da yayyafin da ake yi a Abuja suna rike da kwallaye da ke  bayyana bukatunsu iri daban-daban a kan wannan al’amari da aka dade ana jan daga a kansa. Mata dai na cikin dubban mutanen da ke wannan zanga-zanga a matsayin matsin lamba da suke yin a ganin an dama da su, suna masu koken cewa tsofaffi sun mamaye fagen siyasar Najeriya musamman matsala ta siyar uban gida. A baya dai ana hangen an gwada matasa ba’a kai ga samun biyan bukata ba.

Nigeria - Jugenddemonstration not too young in Abuja (Uwais Abubakar Idris)

Masu zanga-zanga da ke neman a rage shekarun neman takara

 

Akwai dai shugabanin kungiyoyin kare hakin jama’a da suka fito kaman su farfesa Chidi Idiankalu:

‘’Ba abin mamaki bane mu rasa samun nasarar wannan gangami a bana ba, ko a badi ko ma badin badada, amma wannan ba abinda zamu yi wasa da shi bane, domin makomar kasar mu Najeriya muna son ganin matasa su kame madafun iko su shiga siyasa domin su rike makomar mu’’

Nigeria Proteste gegen Muhammadu Buhari in Lagos (DW/S. Olukoya )

Masu zanga-zana a Najeriya

Majalisar datawa dai ta turo wakilanta da suka yi wa masu zanga-zangar jawabi a hanzarce suka koma karkashin jagoranci sanata Dino Melaye, bisa alkawarin cewa, majalisar na duba al'amarin don rage shekarun ‘yan takara zuwa shekaru 35 ga shugaban kasa, shekaru 30 ga sanata yayin da shekru 25 ga dan majalisar wakilai. Abin jira a ganin shine in majalisar ta amince da rage shekarun takara ko ‘yan majalisun jihohi za su bi sawu ko kuwa za’a shiga yanayi na rijiya ta bayar guga ta hana.