Matasan Biafra sun sace jirgi a yankin Cotonou | Siyasa | DW | 04.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matasan Biafra sun sace jirgi a yankin Cotonou

Ana kallon kamen jirgin ruwa na Leon Dias a matsayin sabuwar barazanar da ke iya bude sabon babi a cikin rikicin rashin tsaron da ke neman gagarar Kundila a Najeriya.

Kama daga Boko ta Haram ya zuwa tsagerun yankin Niger Delta da suma ke neman farfadowa da fasa bututun mai dai, lamura na neman cabewa ga gwamnatin da ta zo bisa alkawarin kawo karshen matsaloli na tsaro amma kuma ke lokarin garar Kundila. Na baya baya dai na zaman matasan da ke fafutukar sake farfado da Jamhuriyar Biafra da suka share wata da watanni su na ta zanga-zanga, yanzu haka kuma suka bullo da sabon launi na fafutuka inda suka yi garkuwa da wani jirgin ruwa.

Nigeria Onitsha brennende Reifen Biafra Konflikt

'Yan kungiyar IPOB kan yi kone-kone da nufin yin matsin lamba ga hukumomi kan a saki shugabansu

Gungun matasan da suka yi garkuwa da jirgin dai sun nemi gwamnatin Najeriya da ta saki jagoransu da ke daure a Abuja inda ya ke fuskantar sharia. Matasan na IPOB dai sun yi barazanar tarwatsa jirgin in har bayan tsawon makonni biyu Abujar ba ta kai ga amincewa bukatar tabbatar da yancin na Nmandi Kanu ba.

Ana dai kallon kamen jirgin na Leon Dias dai a matsayin sabuwar barazanar da ke iya bude sabon babi a cikin rikicin rashin tsaron da ke neman samun wajen zama cikin kasar. Duk da cewar dai wasu a cikin 'yan kungiyar sun zare hannunsu a cikin garkuwa da jirgin dai, kamen na nuna alamun jan aikin da ke gaban mahukuntan kasar da ke shirin fafutukar kwantar da tada kayar baya a sassan kasar daban-daban.

Nigeria Onitsha Vertreter der Organisation zur Abspaltung von Biafra MASSOB

Zanga-zanga ta masu rajin girka kasar Biafra ta game sassa daban-daban na kudu maso gabashin Najeriya

To sai dai kuma a tunanin Ahmed Babba Kaita da ke zaman dan kwamitin harkokin tsaro a majalisar wakilan Najeriyar gwamnatin kasar ba ta da zabi face murkushe duk wani tsarin da ke barazana ga dorewar kasar wuri guda a halin yanzu. To sai dai kuma a tunanin Dr Kole Shettima da ke zaman shugaban cibiyar inganta dimokradiyya da cigaba da ke Abuja, mafita ga gwamnatin na ita ce bullo da dabaru na dauke hankali na matasan da ke a tsakiyar rigingimun kasar a halin yanzu.

Sauti da bidiyo akan labarin