1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasan Afirka na neman damar taka rawa cikin harkokin siyasa

December 27, 2012

Majalisar dokokin matasan Jamhuriyar Nijar ta yi zama a birnin Dosso, inda ta mayar da hankali kan muhawara bisa matsalolin ilimi da halin rayuwar matasa.

https://p.dw.com/p/179i4
Majalisar dokokin Jamhuriyar NijarHoto: DW

Majalisar dokokin matasan Jamhuriyar Nijar ta yi zama a birnin Dosso, inda ta mayar da hankali kan muhawara bisa matsalolin ilimi da halin rayuwar matasa a cikin ƙasar da ke yankin Yammacin Afirka.

Yayin bikin buɗe taron, shugaban majalisar Hassan Garba ya yi nuni da matsaloli da matasan ƙasar ke fuskanta musamman yadda ake samun jinkiri wajen buɗe makarantu, da wasu tarin matsalolin da matasan ke fuskanta wanda su ka haɗa da rashin aiki, saboda yadda ake samun waɗanda su ka kammala karatu amma ke ci gaba da zaman kashe wando. Wannan ya sa waɗanda su ka halarci taron kira ga gwamnati ta ɗauki mataki akai, domin rashin aikin matasa na janyo illoli masu yawa cikin ƙasa.

Schule in Grand Bassam
Hoto: picture alliance/ausloeser-photographie

Matasa mata da su ka halarci taron, sun bayyana wasu matsalolin waɗanda su ke fuskanta a rayuwar yau da kullum, kamar yadda wata daga cikin 'yan majalisar matasan ke cewa, sun haɗa da auren dole, da kuma auren yara ƙanana. Sun ɗora wannan matsala kan iyaye, musamman wajen son abun duniya.

Ita wannan majalisar dokoki ta matasan Jamhuriyar Nijar, akwai reshen 'yan majalisu na ƙasa da ke kula da ita da kuma bayar da horo. Kuma ɗan majalisa Idrissa Maidaji ke shugaban wannan rukuni, ya kuma halarci taron na birnin Dosso. Ya bayyana mahimmancin majalisar ta matasan, saboda yadda ake horas da su matakan tsara dokoki, da yadda matasan ke da ƙarfin tunkaran wasu manyan jami'an gwamnati, domin sanin matakan da ake ɗauka na inganta rayuwar matasa a cikin ƙasar.

Yayin da matasan na Jamhuriyar Nijar ke tattauna matsalolin da su ke fuskanta tare da neman hanyoyin shawo kansu, a Tarayyar Najeriya kokawa matasan su ka yi, bisa yadda ake mayar da su saniyar ware game da tafiyar da lamura a cikin ƙasar.

Arbeitslose afrikanische Männer sitzen auf einer Mauer, Germa, Libyen
Hoto: picture-alliance/dpa

A cikin nahiyar Afirka matasa na ci gaba da fuskantar matsaloli, saboda yadda cikin ƙasashen galibi manya ne ke da ta cewa, a wasu wurare matasan kan kasance 'yan bin umurni ne kawai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani