Matasa da ke yakin yaduwar HIV/Aid | Himma dai Matasa | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Matasa da ke yakin yaduwar HIV/Aid

Wata hadakar kungiyar matasa a Najeriya ta dukufa don horar da mata masu zaman kansu hanyoyin rungumar kananan sana'o'in hannu a yunkurinsu na karesu daga cututtuka

Honorable Nehemiah Madugu shine dai shugaban tsare-tsaren kungiyar da aka sani da "Youth Network on Hiv/Aids in Nigeria" wadanda suke horar da mata masu zaman kansu hanyoyin rungumar kananan sana'o'in hannu, domin daina sana'ar karuwanci

"Mun lura da cewa halin da wadannan mata ke ciki, abun tausayi ne kuma a kullum muna da labarin irin hatsarin rayuwar da suke ciki. Hanyar ceto su ita ce kawai a fara horar da su, kananan sana'o'in hannu daban-daban, domin su zamo masu dogaro da kansu, don canza masu rayuwa daga tsohuwar sana'ar ta su ta karuwanci zuwa wata sabuwa"

A wani binciken da hadakar kungiyar matasan ta gudanar ta gano cewa, Mutuwar iyaye da kuma rashin taimakawa marayu, tare da karancin aikin yin da ke addabar matan, hadi da auren dole sune daga cikin matsalolin da ke tursasa 'yan mata shiga harkan karuwanci a kasar.Dayawa daga cikin matan da ke gudanar da wannan harka, wadanda suka kwashe shekaru da damar gaske a cikin sana'ar, sun bayyana irin halin kuncin da suke ciki, kamin zuwan su daukar wannan horo. Inda dayansu ta ce "Rayuwar da muke ciki, rayuwa ce mara kyau, domin ko makiyinka ba za ka so ya shiga wannan harkan ba, domin a kullum muna ganin walakanci ta hanyoyi daban-daban"

Jihar Kaduna dai ta kasance daya daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da masu yawan ciwon HIV/Aid, kuma yawan kananan yara da ke fama da cututtuka da suka dauka daga iyayen su na zama wata babbar barazana ga bangaren kiwon lafiyar kasar.

Sauti da bidiyo akan labarin