Matan Jamhuriyar Nijar sun yunkuro a fagen siyasa | Siyasa | DW | 02.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matan Jamhuriyar Nijar sun yunkuro a fagen siyasa

Mata a Jamhuriyar Nijar sun tashi tsaye domin shiga gaba a harkokin siyasa yayin da zabukan kasa baki daya ke tafe a shekara mai zuwa ta 2016.

Wählerin im Wahllokal in Tahoua Niger

A yayin da ake dab da shiga manyan zabubuka a Jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin matan kasar ne suka sha damarar tsayawa takara har ma da tsaida wasu 'yan uwansu mata takara domin kawo karshen rakiyar da suka ce suke yi wa 'yan siyasar kasar inda da zarar dadi ya zo 'yan siyasa kan gudu su bar su.

Niger Frauen vor Wahllokal in Tahoua


Hajiya Rabi Oumarou daya daga cikin jiga-jigan kungiyoyin matan da suka ce sun gaji da hattara sa ba tare da sun ga kaho ba, bisa la'akari da dimbin alkawullan da maza musamman 'yan siyasa ke yi masu inda sukan shafe bakunan matan da mai da zarar mulki ya samu batun cika alkawullan mata kan zama tamkar an shuka dusa.

Kimanin kashi 52 cikin 100 na al'umar Jamhuriyar Nijar mata ne sai dai wahalhalun dawainiyar gida ko zuwa daji don itace ga mazauna karkaka ya kara saka matan hatta ma wadanda ke zaune a birane da suka san dadin siyasa a cikin wani mawuyacin yanayi wanda a tsawon tafiyar demukradiyar Nijar yau shekaru 25 ba a samu wani dogon sauyin ba inji matan duk da yawan dimbin alkawullan da 'yan siyasa ke yi masu.

Sauti da bidiyo akan labarin