Matan da aka kwato a Sambisa suna Yola | Labarai | DW | 04.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matan da aka kwato a Sambisa suna Yola

Daruruwan yara da mata da sojojin Najeriya suka kubutar daga dajin Sambisa sun bayyana cewa an yi musayar wuta da mayakan Boko Haram kafin a kwatosu.

Akalla mata uku sun rasu bayan fashewar wasu bama-bamai sannan wasu tankunan yaki suka hallakasu a yunkurin da sojan Najeriya suka yi na kubutar da su daga hannun mayakan Boko Haram, kamar yadda daya daga cikin matan da aka yi garkuwa da su ta bayyana a jiya Lahadi.

Wannan rasa rayuka dai ya faru ne a dajin Sambisa lokacin da jami'an sojan Najeriya suka kubutar da daruruwan mata da yara a yankin Arewa maso gabashin kasar ta Najeriya da rikicin ta'addancin ya yi kamari.

A ranar Lahadi na sojojin na Najeriya suka bayyana cewa an dauki mata da yara 275 zuwa wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa. A cewar jami'an wadanda aka kubutar na cikin hali na kuncin rayuwa da ke bukatar kulawar musamman ta fannin abinci da lafiya.

Fiye da mata da yara 700 ne dai sojojin na Najeriya suka kubutar a wannan daji na Sambisa a mako guda da ya gabata, abin da ke kara karfin gwiwa na ganin an kubutar da yaran nan 'yan makarantar Chibok da mayakan na Boko Haram suka yi garkuwa da su sama da shekara guda ke nan.