1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin karshe na tattauna nukiliyar Iran

July 3, 2014

Tattauwar da ke samun halartar wakilan kasashe biyar masu zaunanniyar kujera a komitin sulhu da Jamus, na da nufin kawar ko tabbatar da zargin da ake wa Iran.

https://p.dw.com/p/1CUqt
Ashton und Zarif Atomgespräche 14.05.2014
Hoto: Reuters

A wannan Alhamis dince aka shiga matakin karshe kuma mai hatsari da sarkakkiya a tattaunawar warware rikicin nuliyar Iran a birnin Vienna kasar Switzerland. Tattaunawar wadda ke gudana da wakilan kasashe biyar masu zaunanniyar kujera a MDD da Jamus, za ta gudana zuwa ranar 20 ga watan Juli da muke ciki, inda daga nan ne za'a tantance ko Tehran na kokarin mallakar makaman nukiliya.

Da halin da ake ciki na masu tayar da kayar baya a Iraki da yakin basasar Siriya dai, wannan mataki zai taimakawa Iran da kasashen yammaci samun samun kyakkyawar danganata, a daidai lokacin da yankin gabas ta tsakiya ke kan tsini na barazanar fadawa yaki. A yayin da sabanin haka, zai iya haifar da rashin jituwa da barazanar yaki, inda Amurka da Izraela suka ce za su iya yin amfani da karfin soji.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya ce, kasarsa na da damar amfani da makonni uku masu zuwa wajen kafa tarihin da za'a jima ba'a manta ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman