Matakin Cuba na gyara dangantaka da Amirka | Labarai | DW | 12.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Matakin Cuba na gyara dangantaka da Amirka

Cuba ta ce ta saki fursunoni 53 da ta ke tsare da su saboda dalilai na siyasa bayan da ta yi wa Amirka alkawarin yin haka a wani matakin na kyautata dangataka tsakaninsu.

A karshen mako ne dai mahukuntan na Cuba suka kammala sakin mutanen, batun da ya sanya Washington a wannan Litinin din nuna gamsuwarta da wannan mataki da Havana ta dauka.

Wasu jami'an gwamnatin Amirka da suka tattauna da kamfanin dillancin labarai na Reuters bisa sharadin sakaya sunayensu sun ce nan gaba fadar mulki ta White House za ta mika sunayen mutanen ga majalisar dokokin kasar don shaidawa duniya ko su waye su.

Amirka da Cuba dai sun kwashe shekaru kimanin 50 suna zaman doya da manja to sai dai a dan tsakanin nan bangarorin biyu sun himmatu wajen maido huldar jakadanci tsakaninsu.