Matakan tsaro gabannin zaben Afghanistan
April 2, 2014Yayin da ya rage kwanaki kalilan kafin gudanar da zaben gama-gari a kasar Afghanistan, hankalin mahukuntan kasar yanzu haka ya karkata wajen girka matakan tsaro domin dakile yunkuri na zub da jini a lokutan zaben.
Tun bayan sanya ranar zaben ne dai aka samu karin tashe-tashen hankula da hare-hare irin na kunar bakin wake musamman ma dai a ofisoshin hukumar zaben kasar da ke sassa daban-daban na kasar, hare-haren da kungiyar nan ta Taliban su ka sha ikirarin aiwatarwa saboda adawar da suka ce su na yi da zaben.
To sai dai duk da wannan matsala da ake fuskanta, 'yan siyasa da dama a kasar na cigaba da yakin neman zabensu, zaben da ake ganin zai kasance cike da rudani duba da yadda jami'an hukumar zaben kasar suka yi korafi cewar 'yan siyasa da jami'an gwamnati na yi wa aikinsu katsalandan.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Ummaru Aliyu