1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan sulhu a rikicin Ukraine

Yusuf BalaDecember 24, 2014

Ba a dai bar kafafan yada labarai ba kaiwa ga ginin gwamnatin da ake wannan tattaunawa, abin da yasa ake ganin sai a zaman da za a yi a ranar juma'a za a ji sakamakon tattaunawar.

https://p.dw.com/p/1E9oZ
Ukraine Friedensverhandlungen in Minsk
Hoto: picture-alliance/dpa

An soma wata tattaunawar zaman lafiya da ke da muradin ganin an samar da sulhu tsakanin dakarun sojan gwamnati da 'yan aware masu samun goyon bayan Rasha a yau Laraba.

Cikin batutuwan da ake son tattaunawa a kansu akwai batun janye manyan makaman yaki da musayar firsinonin siyasa.

Da yammacin yau ne dai wakilai daga bangarorin na Rasha da Ukraine da na kungiyar hadin kan tsaro a tsakanin kasashen Turai dana 'yan aware suka hallara a wurin tattaunawar wato Belarus. Ba a dai bar kafafan yada labarai ba kaiwa ga ginin gwamnatin da ake wannan tattaunawa.

Nan gaba kuma a ranar Juma'a za a sake wata tattaunawar wacce Valeriy Chalyi, mataimakin shugaban ma'aikata a gwamnatin kasar ta Ukraine ke cewa a ranar ce zaa ji cikakken sakamakon tattaunawar.